Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Motar Haya Ta Murkushe Wata Dalibar Jami’a A Jihar Osun

Published

on

Mota kirar Bas ta haya ta murkushe wata dalibar jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife cikin Jihar Osun, mai suna Chiwendu Ebenezer, a yankin Mayfair. Majiyarmu ta  labarta mana cewa, Chiwendu ta na kan hanya ta zuwa sayan shawarma ranar Litinin lokacin da motar bas din ta murkushe babur din da ta ke kai. Yayin da dan acaban ya tsallake rijiya da baya, bas din ta bi ta kan Chiwendu. An bayyana cewa, an garzaya da ita zuwa cibiyar shan magani na jami’ar, inda daga baya a ka garzaya da ita zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo, inda a nan ne likita ya tabbar da mutuwar ta.

Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Jude ya bayyana cewa, ya na daya daga cikin mutanen da su ka taimaka mata lokacin da lamarin ya afku. Ya ce, “abinda na ji daga wurin mutane dai, ta hau babur din ne domin zuwa sayan shawarma a yankin Mayfair, inda motar bas din ta samu kwacewar birki ta murkushe babur dinsu. Dan acaban ya tsira, amma ita kuma ta mutu.

“Mutane sun taimaka an kai ta cibiyar shan magani da ke jami’ar. Lokacin da a ka isa wurin, nan take a ka garzaya da ita asibitin koyarwa na jami’ar Obafemi Awolowo, inda a nan ne lititan da yak e bakin aiki ya tabbatar da mutuwar ta.”

Wata aminiyar marigayyan wacce ta nemi a sakaye sunanta ta bayyana cewa, Chiwendu ta mutu ne sakamakon mummunar rauni da ta samu. Ta kara da cewa, “na samu labarin lamarin ne daga bakin kawarmu cewa, ta yi hatsari kuma har an kai ta asibiti, lokacin da na isa asibitin da misalin karfe bakwai na yamma, ta riga ta mutu. Na ziyarci dakin ijiye gawarwaki inda a ka kai gawarta, na samu an rufe mata hannuwa, kafa da kuma fuskanta. “A bayanin da na samu daga wajen ma’aikatan lafiya, sun bayyana min cewa, ta rasa jini mai yawa sakamakon wannan hatsari, kuma shi ne ya yi sanadiyyar mutuwar ta.”   

Jami’in watsa labarai na jami’ar Obafemi Awolowo, Abiodun Olanrewaju, lokacin da ya  ke jajantawa iyalanta ya bayyana cewa, jami’ar ta samu labarin hatsarin Chiwendu, kuma ta mutu lokacin da likita ya ke kokarin ceton ranta.   
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!