Connect with us

MAKALAR YAU

Ni Na Kowa Ne Kuma Ba Na Wani Ba!

Published

on

Shekara kwana, in ji Bahaushe. Kamar jiya ne, shekara hudu da su ka gabata a 2015, a rana mai kamar ta yau aka rantsar da shugaba Buhari a matsayin zababben shugaban kasar na Nijeriya, shugaba na farko da ya kada wani shugaba mai ci a tarihin siyasar kasar. Ba na jin akwai wata rana da a tsawon tarihin wannan kasa wadda akasarin yan kasar su ka nuna farin ciki da kyakkyawan fata ga samun sabuwar Nigeria wadda su ka dade su na muradi, kuma wadda su ka yi ta begen ganinta tun daga shekara 1984 lokacin da su Babangida su ka hambarar da Buhari daga mulkin soja.

A wannan rana Buhari ya yi jawabi wanda ya sosa wa mutane zuciya ya kuma basu kwarin gwiwar cewa lalle akwai alamun za’a sami canjin da aka dade ana fafutuka. Musamman kalaman Buhari da ya yi cewa “Ni na kowa ne kuma ba na wani ba”. Talakawa sun yi tsalle da murna da jin wannan kalami domin Babban burinsu shine na ganin cewa an yi maganin rashawa da cin hanci a kasar, abinda ya hana kasar motsawa saboda kusan kowa ya na da hannu ta wannan fuska ko waccan don haka an kasa samun wanda zai iya tsawatarwa balle ya hukunta.

Na yi imanin cewa a wannan rana, miliyoyin yan Nigeria sun yi barci da minshari, kamar yadda ni ma na yi, tare da kyakkyawan fatan cewa Buhari idan ya yi Magana ba zai saba ba ko kuma ya gaza aikatawa saboda ba ya tsoron kowa. Musamman a wannan lokaci kasar ta sami kanta cikin mummunan halin da ba ta taba samun kanta ba. Farashin mai ya fadi warwas, yan Boko Haram na cin karensu babu babbaka domin sun karbe kusan kananan hukumomi sama da ashirin a tarayyar Nigeria. Ko’ina sai bama-bamai ke tashi a arewacin Nigeria kama daga masallatai, coci-coci, kasuwanni da tashohin mota. Harkokin kasuwanci da na noma sun tsaya cak.

Daya daga cikin abubuwan da Buhari ya fara aiwatarwa shine na umartar rundunar sojojin Nigeria su yi kaura zuwa arewa maso gabas domin tunkarar Boko Haram kai tsaye. Cikin yan watanni sai kararrakin tashin bama-bamai ta fara raguwa, wutar lantarki ta fara samuwa, sakamakon fara amfani da asusun ajiyar gwamnatin tarayya na bai daya (TSA) sai ga lalitar gwamnati ta fara habaka. Duk da kiraye kirayen da masana tattalin arziki su ka yi ta yiwa Buhari na ya rage darajar Naira ya yi kunnen uwar shegu da su kuma ya fito da tsarin bawa bankuna kudaden canjin dala kai tsaye duk sati abinda ya yi gagarumin tasiri wajen tsai da faduwar Naira da kuma farfado da tattalin arzikin kasar yadda ta fice daga koma baya tattalin arziki (recession).

Alamu ta ko ina na nuna cewa dai kwalliya ta fara biyan kudin sabulu. Katsam sai mu ka ji an yi waje da Buhari zuwa Ingila sakamakon shekar guba mai tsananin muni wadda a ka tura ta cikin bututun na’urar sanyaya daki. Cikin kankane lokaci talakawan Nigeria su ka dimauce da dukufa wajen addu’o’i da fatan Allah ya ba shi lafiya. Tsoro ya kama jama’ar kasar saboda kamar tarihi zai maimaita kansa a lokacin Yar Adua. Kama-kama sai da Buhari ya share kimanin watanni uku a kwance a asibitin Ingila amma Allah ma ji rokon bayinsa sai kawai mu ka ji cewa ya sami lafiya kuma zai dawo ya ci gaba da aiki.

Buhari ya je gaban majalisar dattawa inda ya yi dogon jawabi na kimanin awa biyu, abinda ya tabbatar wa da kowa lallai ya sami cikakkiyar lafiya fiye da ma kafin lokacin ya sami wannan lalura. Saboda ingancin lafiyar sa, sai yan adawa da makiya su ka fara yada cewa ai ba Buhari ba ne wani mutumin Sudan ne mai kama da shi ya ke sojan gonarsa.

A zato na kasancewar Buhari ya leka bakin kabari, daga dawowarsa zai gane cewa rayuwa fa aro ce daga mahalicci yadda a kwanne lokaci ya na iya karbe abarsa. Duk wanda ya leka lahira ya dawo ai ya kamata a ce ya mai da hankali wajen yin abinda ya kamata kawai ba tare da tsoro ko la’akari da wani abu ba. Amma sai ga Buhari ya ci gaba da tafiyarsa ta lakai-lakai game da maganar cin hanci da rashawa. Domin ya tafi ya bar rigimar sakataren gwamnatinsa Babachir wanda kwamitin mataimakinsa ke bincika kuma su ka tabbatar da laifinsa a cin hanci da rashawa, amma sai gashi har izuwa yau, zance na balbalcewa a kotu. Na san wadanda ba su yarda Buhari na laifi ba, za su yi karaf su ce ai bashi da iko kan alkalai. To mu dauki matsalar Professor Usman, wanda ya bar rayuwa ta wadata da jin dadi da kima a Amurka ya zo ya karbi aikin hukumar inshorar lafiya. Daga zuwan wannan mutum cikin kankanin lokaci sai gashi ya fara canza akalar yadda ake tafiyar da hukumar tare da fito da tsarin da zai tabbatar da yadda kowanne talaka zai iya cin gajiyar tsarin. Professor ya gano gungun dillalai (HMO’s) da su ka shake ma’aikatar yadda idan gwamnati ta basu kudade ba sa biyan asibitoci sai su rike kudaden, abinda ke kawo wa wadanda ke cikin tsarin tsaiko na rashin samun kulawa sosai. Ya fara yakar wannan gungu ta hanya hana su kudade ba tare da shaidar sun biya na bay aba, amma da ya ke akwai gagga-gaggan ma’aikatan lafiya da su ke da wadannan kamfuna na HMO’s su ka yi kutu-kutu sai da aka dakatar da shi da sahalewar fadar shugaban kasa.

A shekarar farko ta mulkin Buhari mun ga yadda a ka kama Sule Lamido da dansa a ka kai su kurkuku bisa tuhumar cin hanci, amma bayan bada belinsu yanzu shekara uku kenan ba ka sake jin maganar an maida su kotu ba. Haka nan shari’ar Shekarau da Aminu Wali, Danjuma Goje da ta su Fani Kayode da Olise Metu duk sai tafiyar hawainiya su ke. Hakika an yanke wa Joshua Dariye da Jolly Nyame hukuncin shekaru a kurkuku, amma kada mu manta cewa tun 2011 su ke a kotu. Idan har Buhari ba zai iya tursasa Alkalai ba, to kada mu manta cewa kuma fa ya na iya bijere musu a shari’o’in da ya ke da muradi domin mun ga yadda kotuna su ka umarci a saki Sambo Dazuki da Sheikh Zazzaki amma ya yi biris da wadannan umarni na kotuna. Shin maganar Buhari cewa “shi ba na kowa bane” akwai gaskiya kuwa? Musamman idan mu ka yi la’akari da yadda karara ya nuna cewa shi na Ganduje ne, domin duk da kafa sunansa a tsawon shekaru 50 na yaki da cin hanci da rashawa, sai ga shi an kawo bidiyon Ganduje yana karbar daloli amma ko da sau daya Buhari bai taba fitowa ya yi Allah wadai da lamarin ba. Hasali ma da a ka fara yi masa zance a France sai ya bige da yabon gwamnatin Ganduje cewa ta na aiki. Sannan a lokacin hirarsu da Kadaria daf da zabe sai kokarin kare lamarin ya yi da cewa ba shi da sahihancin bidiyon, wanda EFCC daga baya ta tabbatar da shi amma ba tare da daukan wani mataki ba.

Idan akwai wani dan siyasa da ya kamata ya martaba muradin masu kada kuri’a a Nigeria bayan Buhari ne domin karo uku ya na shiga zabe ba nasara amma sakamakon an yi zabe na gaskiya kuma Jonathan ya dubi masalahar kasa ya yarda da kaye, shine ya ba shi damar zama shugaban kasa. Amma sai gashi da sahalewarsa an yi wa mutanen Kano kwacen zabe. Kowa ya ga yadda Buhari ya bada oda kafin zaben shugaban kasa cewa a harbi duk wanda ya saci akwatu, kuma wannan furuci na sa ya yi matukar tasiri wajen samar da zaben shugaban kasa mafi tsafta a tarihin Nigeria yadda babu rigingimu da ta’addanci kuma masu kada kuri’a su ka zabi abinda su ke so. Amma a Kano an je an tarwatsa mazabar Gama kuma aka yi amfanida wannan ta’addanci wajen sake zabe, wanda kowa ya ga abinda a ka yi amma Buhari ko uffan bai ce ba kawo yau.

A baya ni da kai na na yi wa Aisha Buhari raddi saboda irin surutun da ta ke yi game da me gidanta saboda a zato na ko kasancewar ya hana ta ofishin first lady da kuma hana ta babakere a cikin gwamnati kamar yadda ta yi ta saka mutanenta a lokacin PTF, shine dalilin da ya sa ta ke caccakarsa. Ko a satin da ya gabata ta caccaki mijin na ta cewa gwamnatinsa ba ta yi arewa komai ba wajen sassauta talauci, abinda ni ma na yarda da shi a yanzu. Daga dukkan alamu akwai kanshin gaskiya wajen korafe-korafenta.

Mun ga yadda cikin dan kankanen lokaci zuwan Buhari, duk da cewa yan Boko Haram sun mamaye arewa maso gabas kuma yankin arewa ba ka jin komai sai tashin bama-bamai a masallatai, coci-coci, kasuwanni da tasashin mota, amma umartar rundunar soja ta yi kaura zuwa yankin ya bada damar dakile Boko Haram, amma sai ga shi a yau ta’addanci da satar mutane ya dawo ya yi katutu a yankin arewa maso yamma. Bayan daidaita Zamfara yanzu Katsina, jihar da shugaban kasa ya fito, ita ta dauki harami yadda ake sace mutane ta ko’ina tare a far ma kauyuka ana kashe mutane babu gaira babu dalili. Hanya mafi mahimmanci a arewa wadda ita ce cibiyar da ta hada yankin arewa da na kudu, wato titin Kaduna-Abuja ya kasance da rana tsake sai a tare hanya a dauki mutane a kashe na kashewa. Kuma ba mu manta da cewa lokacin da ake aikin gyaran filin jirgin saman Nnamdi Azikwe na Abuja sai da aka yi tsawon watanni jami’an tsaro na ba shi kulawa da kariya yadda har a ka gama ko kaza ba a dauke ba. A yau masu hannu da shuni sai ta jirgin sama su ke zuwa Abuja yadda matsakaita ke zuwa Kaduna su hau jirgin kasa sai direbobinsu su bi hanyar zuwa Abuja su dauke su a tasha. Shi kansa jirgin saman sai ya sami rakiyar jirgin yaki mai saukar ungulu.

Alamu na nuna cewa Buhari ya gaza, a kullum sai zancensa ka ke ji cewa, zan yi kaza, manya kasa ba sa so na, kasa ta lalace sakamakon rashin tsari na tsawon shekaru da sauransu. Magana ta gaskiya duk shugaban da a kullum ya ke kasa iya amsa gazawarsa sai laluben inda zai dora laifi to hakika ya gaza. A yau ranar da a ka sake rantsar da Buhari a karo na biyu, hakika shi da kansa ya tabbatar da gazawar sa domin ya karbi rantsuwa ba tare da koda godiya ya iya  yi wa mutanen kasa na sake zabensa ba. Amma dai maimakon ya maimaita zancensa na cewa “Shi na kowa ne kuma ba na kowa ba” gara ma da yayi shirun.

A karshe ina so kira ga Buhari ya gane cewa a yau a duk fadin duniya babu wani shugaba a wannan karni da al’ummarsa su ka nuna masa tsagwaron soyayya da aminci kamar sa ba. Domin ko Mandela bai sami cikakkiyar soyayya irin ta Buhari ba, sai dai kawai ya fi Buhari kima saboda ya gama da duniya lafiya. Matukar Buhari ba ya son ya yi faduwar bakar tasa, wajibi ne a wannan Zango na shekaru hudu masu zuwa ya jajirce wajen nu na ba sani ba sabo game da cin hanci, domin shi ne babbar matsalar mu. Duk da cewa kowa ya amince da cewa shi ba ya cin hanci amma ina amfani idan ya na zuba ido wadanda ke kewaye da shi su na yi? Shin Allah ba zai tambaye shi ba? Duk abinda zai yi, bayan shekara hudu idan ya gaza a cin hanci, tsaro da tabbatarwa a aikace cewa shi din fa na kowa ne kuma ba na wani ba, hakika tarihi ba zai raga masa ba, ballantana ya tuna da shi a matsayin Mandelan Nigeria.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!