Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Gurfanar Da ‘Yan Kungiyar Asiri Guda Tara A Kotu

Published

on

A cikin makon nan ne, ‘yan sanda su ka gurfanar da mutum 9 wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne a babban kotun Jihar Ogun, wacce ta ke da zama a garin Ota. Wadanda a ke zargin dai ssu ne; Sulaimon Ganiyu dan shekara 19, Amechi Goodluck dan shekara 19, Akonmosa Boluwatife dan shekara 19, Jeelili Adebowale dan shekara 19, Babatunde Akeem dan shekara 19, Riliwan Owolabi dan shekara 18, Segun Olarewaju dan shekara 18, Salawu Azeez dan shekara 18, sai kuma Azeez Kazimu mai shekaru 18. Wadanda a ke zargin dai su na fuskantar hukuma guda uku wadanda su ka hada da tayar da hankulan al’umma, hada kai domin aikata laifi da kuma tayar da zaune-tsaye. Wadanda a ke zargin sun musunta laifin da a ke tuhumar su.

Lauyan ‘yan sanda mai gabatar da kara, Sajan Abdulkareem Mustapha ya  bayyana cewa, wadanda a ke tuhumar sun aikata wannan laifi ne a ranar 3 ga watan Mayu, a yankin Plaza da ke cikin garin Ota ta Jihar Ogun. Mustapha ya zargi wadanda a ke tuhuma da kafa kungiyar asiri mai suna Orikankere Confraternity. Ya bayyana wa kotu cewa, wadanda a ke tuhuma sun hada kai wajen tayar da hankulan al’umma, kamar jawo rikici da kuma shan muyagun kwayoyi a cikin jama’a. Lauyan ya kara da cewa, wannan laifi ne wanda ya saba wa sashi na biyar da 516 na dokar manyan laifuka ta Jihar Ogun wanda a ke yi wa garanbawul ta shekarar 2006.

Alkali mai shari’a Mista Mathew Akinyemi, ya bayar da belin wadanda a ke hukuma a kan kudi naira  300,000 ga kowannan su tare da mutum biyu masu tsaya musu. Akinyemi ya bayar da umurnin cewa, mutum biyun masu tsaya musu, to su kasance su na zaune ne a kusa da kotu, sannan kuma ma’aikata ne. Ya kara da cewa, su kasance su na da takardar shaida na biyan kudin haraji na gwamnatin Jihar Ogun. Ya dage sauraran wannan kara har sai ranar 17 ga watan Yuni.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a ruwaito wani lamari irin wanna, inda ya bayyana cewa, an gurfanar da mutum bakwai wadanda a ke zargin ‘yan kungiyar asiri ne a gaban kotun Ota. Ana dai tuhumar su ne da laifuka wadanda su ka shafi kisan kai da kuma na tada hankulan mutane.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: