Connect with us

SIYASA

Za Mu Dauki Matakin Ba-Sani-Ba-Sabo Kan Matasan Da Ke Karya Doka, in Ji Gwamnatin Bauchi

Published

on

Gwamnatin jihar Bauchi ta ce, ba za ta lamunci munanan dabi’un wasu matasan da ke karya doka da oda a fadin jihar Bauchi, ta ce, za ta dauki matakin babu-sani-ko-sabo kan masu take doka da karya shi.

A cikin wata kwafin sanarwar manema labaru da gwamnatin jihar ta fitar dauke da sanya hanun Sakataren gwamnatin jihar Bauchi Mohammed Sabi’u Baba, ta ce gwamnatin ta nuna damuwarta gaya kan rashin jituwar da aka samu a tsakanin wasu matasa a ranar Hawan Daushe a cikin kwaryar Bauchi.

Idan za ku iya tunawa mun kawo muku rahoton da ke cewar ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum guda, jikkata ‘yan Tauri 14, da kuma cafke mutum 55 da ake zargi wajen tayar da rigima a tsakanin matasa a lokacin hawan Daushe na wannan shekarar a fadin jihar.

Sanarwar ta gwamnatin Bauchi ce, “A ranar Laraba 5 ga watan Yuni, 2019 Mai Martaba Sarkin Bauchi ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed Abdulkadir,”

Sanarwar ta ce, gwamnatin tana sane da rashin jituwar da ta barke a tsakanin wasu matasa a lokacin da Sarakuna ke kai gaisuwar Sallah wa gwamnan jihar Bauchi a gidan gwamnati, wanda hakan ya haifar da jikkata wasu, “Jami’an tsaro sun yi kokarin shawo kan matsalar da kuma cafke wasu da ake zargi wanda bincike ke ci gaba da gudana yanzu haka.

“Gwamnati tana sane da cewar akwai wasu marasa kishin jihar da suke da hanu cikin lamarin wadanda suke boye da suke son bata wa Gwamnati mai ci suna.

“Gwamnati ba za ta lamunci aikata laifuka na ashsha ba. Babu yadda yadda yadda mu zauna mu zura ido wasu suna kan karya doka da oda mu kyalesu. Don haka, za mu hada hanu waje guda da bangarorin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a jihar nan wajen magance irin wannan lamarin na rashin bin doka da oda,” A cewar gwamnatin.

Sanarwar ta Mohammed Sabi’u tana cewa Gwamnati  za ta tabbatar da wanzar da kare rayuwar jama’an jihar da lafiyarsu, “Hakazalika tana tabbatar wa al’ummar jihar cewar za mu tabbatar da wanzar da zaman lafiya, kare dukiyoyi da rayukan mazauna jihar,” A cewar sanarwar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!