Connect with us

RAHOTANNI

An Gina Sabbin Asibitoci 83 A Jihar Jigawa Cikin Shekara 4

Published

on

Gwamnatin jihar Jigawa ta gina sabbin cibiyoyin lafiya matakin farko guda 83 a shekaru hudun da suka gabata.

Haka kuma gwamnati tana aikin gina sabbin asibitin kwararru guda biyu tare da daga likkafar cibiyoyin lafiya matakin farko da manyan asibitoci masu tarin yawa.

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya sanar da hakan a jawabinsa na bikin rantsuwa karo na biyu. Ya ce, jihar Jigawa tana da cibiyar lafiya matakin farko a kowace mazaba kamar yadda ya yi alkawari a karshen 2017

Gwamnan ya ce, gwamnatinsa ta kara yawan adadin kason kudaden da kashewa a shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara tare da kara yawan cibiyoyin lafiyar kula da shirin daga 22 zuwa 162.

Ya ce, sakamakon bullo da shirin gwajin cuta mai karya garkuwar jiki kafin a yi aure, jihar Jigawa ta yi kasa da yawan masu dauke da cutar zuwa digo uku.

Akan cutar shan Inna kuwa, gwamnan ya ce, jihar Jigawa bata da dauke da cutar polio tun hawan gwamnatinsaa yayinda aka gudanar da zagaye 30 na allurar shan inna tare da yi wa kananan yara miliyan daya da dubu dari bakwai a kowane zagaye.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!