Connect with us

RAHOTANNI

Babu Shugaban Da Zai Samu Karbuwa A Wajen Jama’a Sai Ya Zama Adali – Bojoh

Published

on

Honorable Gambo Tanko Kagara, shi ne tsohon shugaban karamar hukumar Rafi ta jihar Neja. Ya bayyana cewar samun nasara a shugabancin karamar hukumar na shekaru uku bai wuce mayar da hankali kan abubuwan da jama’a ke bukata, ingancin siyasa da kwarjininta ga dan siyasa ya biyo bayan amincewar talakawa a jagorancin ka. A hirarsa sa da wakilinmu Muhammad Awwal Umar, Honorable Bojoh ya bayyana cewar maganar takarasa karo na biyu ya danganta da ra’ayin mutanen Rafi ne.

A ‘yan lokuttan baya karamar hukumar Rafi ta samu kanta a cikin yankunan da suke fuskantar matsalolin masu garkuwa da mutane musamman a bangarorin da ku ke iyakokin da jihohin Kaduna da Zamfara, sanin kowa ka ta ka rawar gani, amma wucewar ka abin yaso sa ke dawo wa. Wasu dubaru kai amfani da su na ganin ka dakushe kaifin wadannan batagarin.

Da farko ina godiya ga Allah da ya ba ni damar da jama’ar Rafi suka jaraba ni a matsayin shugaban karamar hukuma kuma hakan yasa na kai ga rike shugabancin kungiyar shugabannin kananan hukumomi da jiha har tarayya wanda kowa shaida ne akan irin rawar ganin da muka taka bisa gudunmawar da muka baiwa yankin mu da har yanzu jama’ar mu na alfahari da hakan.

Maganar tsaro ba aikin mutum daya ba ne, abu ne da ya shafi kowa, abinda ya kamata ga shugaban al’umma shi nemo hanyar da zai tabbatar da dakile duk wata barazana da ta shafi rayuwa da arzikin jama’arsa.

A matsayin ka na shugaba dole ka hada kai da jami’an tsaro wajen ba su kwarin guiwa dan samun nasarar aikin su ta hanyar taimaka masu da duk wata gudunmawar da suke bukata, akan haka mun taka rawar gani sosai.

Na biyu akwai bukatar hada kai da jama’a wajen samo bayanan sirri domin da irin wannan salon ne kawai za ka iya sani gano batagarin da ke shigo wa cikin jama’a da kuma daukar matakin dakile shi ba tare da su batagarin ko ‘yan ta’addar sun san wadanda ke tsegunta sirrin su ga gwamnati ba.

Hakan kuwa bai samuwa sai da kyakkyawan alaka tsakanin ka da al’ummar ka. A kullun ‘yan ta’adda su kan bullo da dubarunsu haka jami’an tsaro suna sanya ido kullun wajen dakile su, dan haka gwamnati ba iya tabbata gwamnati sai ta iya kare rayuwa da arzikin jama’ar ta. Dan a lokacin da muka rika karamar hukumar Rafi mun yi kokari gaya da goyon bayan jama’a da na jami’an tsaro wanda yasa har yau ake jinjinawa wannan dan bajintar da muka nuna.

Abu na biyu kuma mun dubi halin da mata da matasa ke ciki na rashin aiki da talaucin da suke fama da shi, wanda da taimakon uwargidan gwamnan jiha, Dakta Amina Abubakar Sani Bello ta bullo da shiraruwa wanda mun yi anfani da wannan damar kuma jama’ar mu sun anfana da shi, wanda yanzu haka da daman matasan mu maza da mata da shi ne suka dogara a rayuwar su.

Jama’a na kiran ka da sunan Bojoh mai ruwa, ina wannan sunan ya samo asali kuma me hakan ke nufi.

Lokacin da muka zo karamar hukuma a matsayin zababben shugaban karamar hukuma, a lokacin yakin neman zabe mun fahimci jama’ar mu na fama da matsalar ruwan sha, wanda ta kai musamman matan da ke cikin karkaru kan yi tafiya mai nisa wajen neman ruwan sha, haka yara ‘yan faramare ba sa samun zuwa makaranta kan kari saboda da safe sai sun nemo ruwa kafin a iya wasu ayyukan gida da zai ba su kwarin guiwar tafiya makaranta cikin lokaci.

Karamar hukumar Rafi tana da ward goma sha daya ne, abinda muka fara yi a karon farko shi ne samar da fanfunan burtsatse a dukkanin wadannan ward din ta yadda mata da yara za su samu saukin samun ruwan sha kusa da su, wannan jin dadin ne yasa su matan da kansu suka fara kira na da Bojoh mai ruwa, saboda jin dadin abinda muka yi.

Irin wadannan ayyukan yasa a duk inda na shiga har yanzu da ba na kujerar shugabancin karamar hukuma za ka ji mata da yara na kiran sai Bojoh, wani abu da zai baka mamaki ko a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar tarayya da na gwamnoni da ‘yan majalisar jiha, idan ka tafi runfunan zabe sai ka ji iyayen mata suna fadin a nuna masu jam’iyyar Bojoh, to ka ga ayyukan da Allah Ya ba mu ikon yi, ayyuka ne da suka shiga zukatan jama’ar mu.

A duk lokacin da ka yi aikin alheri a matsayin ka na shugaba dole ne jama’a su nuna sha’awarsu gare ka. Ba yadda dan siyasa zai iya samun nasara sai ya yiwa jama’a abinda suke bukata.

Misali samar da abubuwan more rayuwa ga jama’a, kirkiro hanyar samar da walwalarsu da kyautata wa mata da matasa, ta hanyar dora su akan turbar da zai sa matasa su kaucewa fadawa shaye-shaye, samar da gurabun ayyuka ga matasan da zai sa su iya dogaro da kafarsu wanda hakan ne zai hana su fadawa cikin miyagun halaye.

Bayan kammala babban zaben da ya gabata, maigirma gwamna yace ba zai nada shugabannin riko a yankunan kananan hukumomi ba, hakan ya bashi kwarin guiwar ganin zai yi zaben kananan hukumomi, ya ka ke kallon wannan shirin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!