Connect with us

RAHOTANNI

Gwamnan Jihar Neja Ya Shirya Tafiya Da Dukkan Bangarorin Al’umma –Wanna

Published

on

A dai-dai lokacin da ake shirin shiga zango na biyu na mulkin gwamnatin Neja, jama’a sun fara sanya idanu akan yadda ake kokarin rarraba mukaman gwamnati a jihar.

Alhaji Muhammad Awaisu Wanna yana daga cikin ‘yan gaba gaba na ganin gwamnatin jihar ta nemo wadanda suka can-canta da a baiwa mukamai dan kar a sake komawa inda aka fito. “Ya ce, a baya an samu kura-kurai na nada wadanda ba su san ne ake cewa mukami a mulkin siyasa ba, wanda yasa irin rawar da wadannan mutanen suka taka yasa gwamnatin ta samu tirjiya daga bangaren talakawa, wanda kan hakan su kai ta fama a kafafen yada labarai dan wayar da kan jama’a da neman a wannan karon kar gwamna ya yarda ya sake mai-maita irin wannan Kuskuren na baya.

Alhaji Awaisu ya ce, mu a jihar nan muna kan tsarin karba-karba ne amma duk da hakan akwai mukaman da gwamna ne ke da ikon zabin wadanda yake ganin za su yi masa aiki saboda yarda da amana. Misali mukamin mataimakin gwamna, shugaban majalisa da minista a matakin tarayya da kwamishina a matakin jiha wajibi a rarraba su, idan gwamna ya fito daga Arewa, sai mataimaki ya fito daga yamma ko gabas, haka shugaban majalisa sai ya tafi kudu ko gabas, ya yin kujerar kwamishinoni kuma sai a rarraba a sauran kananan hukumomi dan su samu wakilci a cikin gwamnati.

Idan ana cewar wai gwamna yaki baiwa Zone “B” wannan damar kuskure ne babba, domin lokacin sardauna rabon wannan yankin da su samu mukamin minista sai fa a wannan gwamnatin ne cikakken bagware ya wakilci jihar a majalisar ministoci. Dan haka da kujerar shugaban majalisa ko kujerun kwamishinoni aka hana mu to a lokacin ne zamu fito mu kalubalanci gwamnati, amma kan maganar sakataren gwamnati ko shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da jami’in hulda da ‘yan jarida zuwa sakataren musamman na gwamna ba mu da abin cewa.

Ina kiran jama’ar mu da babban murya su daina baiwa ‘yan a fasa kowa ya rasa damar kafa wata digon cuta a zukatansu, lokacin marigayi Kure ya yi sakatarorin gwamnati har sau biyu duk cewar shi kan shi gwamna Kuren tamkar dan yankin nan ne, gwamnatin Talba ta dauko wanda ma bai san siyasa kuma ba a taka rawar siyasar da shi ba a ya bashi mukamin kwamishina da har ya kai sakataren gwamnati.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!