Connect with us

RAHOTANNI

ITF Ta Fara Kokarin Kawo Karshen Rashin Aikin Yi Ga Matasa

Published

on

Dangane da rashin aikin yi wanda ya addabi mazauna Nijeriya, asusun harkokin kasuwancin na (ITF) ya yi kira ga gwamnatoci kama daga kan gwamnatin tarayya har zuwa na jahohi domin a hada hannu tare da hukumar domin magance matsalar aikin yi da yawancin matasan suke fama da shi.

A wani bangare, kuma hukumar ta ce yanzu haka ta fara horar da matasa sama da  450,000 a cikin shekaru biyu da suka gabata a kasar wanda hakan zai taimaka musu wajen samun kudin shiga a zamantamewar su ta yau da kullum.

Daraktan  hukumar, Joseph Ari shi ne ya bayyana haka a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi a lokacin kammala karatun digiri na 7 na cibiyar harkokin kasuwancin masana’antu na kasa (NISDP).

Ya ce an horar da mutane 11,000 a fadin kasar wasu hanyoyi kamar haka: Walda,Kere-kere, Filasta, ( POP), da kuma daukar hoto, 310 daga cikin wadanda aka koyawa sun fito ne daga jihar Ebonyi.

“Burin mu shine samar da aikin yi ga matasan mu ta Inda za su rinka aikin da basira wajen gudanar a aikin su, kuma cikin wannan shekara muna fatan zasu samar da kayan aikin gona saboda shima babbar hanya ce ta rage yawan masu zaman banza”, in ji shi.

Manajan yankin da ke kula da ofishin na ITF na Abakaliki, Ifeyinwa Mary-Ann Osagie ya lura cewa kasar nan tana fama da mutane wadanda basu da aikin yi kuma kullum sai kara karuwa suke yi, duk da cewa gwamnatin tarayya tana iya bakin kokarin wajen samar da aikin yi.

“Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa a cikin shekara ta 2019 kashi 23.1 bisa dari basu da aikin yi da kuma kashi 16.6 cikin dari basu da abinda za su yi. Duk ka binciken ta bayyana cewa kashi 60 na 100 na ‘yan Najeriya sune kadai suke aiki.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!