Connect with us

RAHOTANNI

Majalisar Kasa Zango Na 9: An Bukaci Zaben Ahmed lawan A Matsayin Shugaba

Published

on

Wasu gungun ‘yan majalisun Dattijai a karkashin wata kungiyar ‘yan majalisun wacce ake kira da, Initiatibe for Leadership Debelopment and Change (ILDC), sun bukaci wakilan majalisar a zaman majalisar na zango na Tara, da su zabi Sanata Ahmed Lawan, a matsayin sabon shugaban majalisar ta Dattawa domin neman ci gaba cikin hanzari.

Wakilan kungiyar suka ce, zaban Lawan a matsayin shugaban majalisar ta Dattawa zai kasance zabe ne na wanzar da hadin kai a tsakankanin ‘yan majalisun da kuma sashen gwamnati da ci gaban Nijeriya.

Cif Ugochukwu Nnam, shugaban kungiyar Sanatocin, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa cewa, zaman doya da manjan da aka yi a majalisa ta 8 a da fadar shugaban kasa ya kawo nakasu ga ci gaban kasar nan.

Ya kwatanta Sanata Lawan a matsayin abin dogaro, kwararren Sanata wanda yake da mahanga iri guda da ta shugaba Buhari, ga ci gaban kasar nan.

“Ina roko a madadin ‘yan Nijeriya ga Sanatocin da su zabe shi domin samun ci gaba da bunkasar Nijeriya.

Shugaban na kungiyar ta ILDC, ya bukaci Sanata Ali Ndume da ya yi koyi da Sanata Danjuma Goje, da ya sauka ya barwa Sanata Lawan, wanda ya ce domin Nijeriya ne.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!