Connect with us

RAHOTANNI

An Karrama Wakilin LEADERSHIP A YAU A Kebbi

Published

on

A ranar Juma’ar da ta gabata ne wata kungiya mai suna Gulma, Lailaba, Alwasa, Tudun Zazzagawa & Sauwa Debelopment Association ta karrama Muhammed Jamil Yusuf Gulma, babban wakilin LEADERSHIP A YAU mai kula da jihohin Sakwkwato, Kebbi da kuma Zamfara a mahaifarsa ta Gulma da ke cikin karamar hukumar mulki ta Argungu a jihar Kebbi.

Da ya ke zantawa da LEADERSHIP A YAU, shugaban wannan kungiyar, Kwamared Yahaya Salihu Gulma, ya ce, “dalilin da ya sa mu ka zakulo irin wadannan mutanen mu ka karrama su shi ne, mu na la’akari ne da irin gudunmawar da su ke bayarwa a bangarorin ayyukansu ne, saboda wadansu su gani su ma su yi koyi da su.

“Duk da ya ke kowa ya sani aikin jarida ya sukurkuce, saboda canjin zamani, amma dai bai sanya Jamil ya kasance daga cikin ’yan barandan ’yan jarida ba, duk wanda su ke ma’abota karatun jarida ya na ganin irin yadda Jamil Gulma ke gudanar da aikinsa na jarida ba sani ba sabo, wanda kowa ya san irin dauki ba dadi da ya ke yi, musamman da marasa gaskiya daga cikin shugabanni, saboda ya yi suna wajen tsage gaskiya komai dacinta. Mun sani babu irin barazanar da bai hadu da ita ba tun kama daga gwamnati zuwa ’yan siyasa.”

Har wa yau dai LEADERSHIP A YAU ta zanta da Jamil Gulma, inda ya bayyana cewa, ya gode wa Allah da har a ka ga amfaninsa a cikin al’umma, wanda har ta kai ga a karrama shi a idon duniya, wannan ba karamin abin jin dadi ba ne da kuma kara ma sa kwarin gwiwa wajen gudanar da aikinsa na jarida.

Ya kara da cewa, “magana ta gaskiya bai kamata a sami dan jarida ya koma dan barandan gwamnati ko kuma wadansu ’yan siyasa ba ko dan-ku-ci-ku-ba-mu ko a same shi ya na tsegunta maganganun ‘yan siyasa, saboda kwadayin abin duniya ba wanda ya na daga cikin abubuwan da su ka zubar da kimar ’yan jarida.

“Kuma bai kamata a sami dan jarida da tsoro ba, kamar yadda mu ka sani duk wanda ya dauki fannin aikin jarida, to ya dauki hanya mai wuya, wacce ya san zai hadu da barazana iri-iri, idan ya ji tsoro shikenan shi an gama da shi, idan kuma ya yi tsayin-daka a kan aikinsa, ba shakka zai cimma nasara.

“Manyan ’yan jarida na duniya da su ka yi suna, mun sami tarihin irin barazanar da su ka hadu da ita, amma da su ka jajirce daga baya Allah ya daga sunayensu.”

Alhaji Abdulnasir Sani Argungu, daraktan yada labarai da harkokin yau da kullum a hukumar gidan talabijin ta jihar Kebbi, ya bayyana cewa, “yadda wadannan matasan su ka yi, ya yi daidai, saboda sun karrama wanda ya cancanta a karrama shi. Mu ne abokan aikin Jamil kuma mu ne mu ka san shi ta bangaren aikinsa, mu ne mu ka san irin gwagwarmayar da ya ke sha kuma bai fasa ba wanda ba shakka ya cancaci a karrama shi.

“Wannan Kuma ba karamar sa’a ya samu ba, saboda bai zama inuwar giginya ba tunda a gidansu a ka karrama shi a idon duniya. Wannan ya na nuni da cewa shi bai bar gida ba.”

Da ya ke tsokaci dangane da wannan karramawar Alhaji Usman Sani mataimaki ne ga mai girma Sanata Dokta Yahaya Abdullahi. Ya bayyana Muhammed Jamil a matsayin sadauki, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen gudanar da aikinsa tsakani da Allah ba sani ba sabo, inda ya ce, duk wanda ke karanta rubuce-rubucensa ya san ba ya jin tsoron fadar gaskiya.

Ya yi addu’ar “Allah ya kara ma sa kwarin gwiwa da cigaba da fadar gaskiya wajen gudanar da aikinsa ya kuma yawaita ma na ire-irensu,” a ta bakinsa.

Taron dai ya sami halartar Nasir Dan’umma, dan majalisa zartarwa na jihar Kebbi, Hon. Musa Muhammed Tungulawa shugaban karamar hukumar mulki ta Argungu, uwayen kasar Gulma, Lailaba, Alwasa. Tungar Zazzagawa da kuma sauran manyan ma’aikatan gwamnati ’yan siyasa da kuma ’yan jarida.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!