Connect with us

KASUWANCI

FAAN TA Rufe Sashen Filin Jirgin Sama Na Murtala Muhammed Sati Shida

Published

on

Hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta kasa FAAN ta sanar da cewa, ta rufe wasu sassa na filin jirgin Murtala Muhammed, inda rufewar ta fara aiki daga ranar 7 ga watan Yunin wannan shekarar.
Janar Manaja ta hukumar dake hudda da alummar gari Uwargida Henrietta Yakubu ce ta sanar da hakan aranar Juama’ar data wuce, inda ta ce, rufewar ta shafi harda kofar Apron 1 da kuma wasu sassan na Tadiway F.
Uwargida Henrietta Yakubu ta ci gaba da cewa, hukumar ta dauki wannan matakin ne don a baiwa yan kwangila damar yin aiki a sabon wajen saukar jiragen sama da ake shirin dangana shi da tsohon gurin tashin jiragen saman.
A cewar Uwargida Henrietta Yakubu, hukmar ta FAAN, tana son ta sanar masu kamfanonin jiragen sama cewa, daga ranar 7 ga watan Yunin wanna shekarar, filin jirgen saman na Murtala Muhammed zata rufe wasu sasaan da suka hada da, kofar Apron 1 da kuma wasu sassan Tadiway F yadda ba yadda wani abin hawa ko mutum da zai iya yin amfni dasu ba har nan da sati shida masu zuwa.
Janar Manaja ta hukumar dake hudda da alummar gari Uwargida Henrietta Yakubu ta kara da cewa, hukumar ta dauki matakin ne don baiwa yan kwanglar da yin aikin damar gudanr da aiki akan sabon gurin saukar jiragen sama don hada shi da tsohon gurin saukar jiragen da a filin jirgin na Murtala Muhammad.
Mahukuntan hukumar ta FAAN ta kuma bukaci goyon baya da hadin kan dukkan wadanda abin ya shafa dasu tattatar sun lura da yanayin zirga-zirgar su a filin jirgin har zuwa lokacin kammala aikin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!