Connect with us

KASUWANCI

Fitar Da Fetur Da Aka Shigo Da Shi Nijeriya Ya Karu – NNPC

Published

on

Kamfanin NNPC ya ce, samfarin man fetur na PMS a ka shigo da shi daga kasar waje ta hanyar shirin kamfanin DSDP na sayar da shi kai tsaye ya karu zuwa litoci miliyan 534.
Har ila yau, NNPC ta janyo kwararrun kamfanoni akan sayar da danyen mai kai tsaye don samar da man a daukacin fadin kasar nan.
A cikin shirin na DSDP, NNPC na rabar da danyen mai duk wata kamar yadda ta tsara a tashoshin jiragen ruwa dake ciukin kasar nan. Man da ake rabarwa, dole ya kasance ingantacce ne da aka samar daga NNPC.
A bisa bayanan da aka samu na kwanan daga NNPC, sun nana cewa, man na PMS da aka shigo dashi cikin kasar nan ta hanyar shirin kamfanin na DSDP ya karu sama da litoci miliayan 500 daga Janairun 2018 and January 2019.
NNPC shi kadai ne yake shigo da PMS cikin kasar nan yau kusan shekaru biyu da suka shige. A bisa fashin bakin da akayi akan adadin na wata-wata aka shigo da man da NNPC yake yi ta hanyar shirin na DSDP ya nuna cewa, a cikin Janairun 2018 Nijeriya ta shigoi da litocin man miliyan 1.464, inda hakan ya karu zuwa litoci biliyan1.998 a Janairun 2019.
Kamfanin na NNPC ya ci gaba da cewa, a Janairun 2019, an shigo da litoci miliyan 1,998.61 na PMS ta hanyar shirin DSDP sabanin litoci miliyan 1, 780.2 na PMS da aka samar a Disambar 2018.
A 2019, litoci miliyan 1,998.61 na PMS aka shigo dashi cikin Nijeriya ta hanyar shirin DSDP, sabanin litoci miliyan 1,780.2 na PMS da aka samar a cikin Disambar 2018.
Shirin na DSDP, kamfanin NNPC yana yin amfani dashoi wajen samar da sauran dangogin man da suka hada da, Kalanzir, Man fetur da kuma Dizil saboda rashin kokari da matatun fetur na kasar nan. Matatun man su ne na garin Fatakwal, Kaduna da kuma Warri.
Jaridar Punch ta ruwaito a kwanan baya cewa, babu ko dingon danyen mai da matatar mai tun Yulin 2018, ganin cewa, man da matatr ta sarrafa na karshe a cikin Yunin 2018.
Har ila yau, matar mai ta KRPC itama bata sarrafa wani danyen mai bat un Fabirairun 2018.
A cewar rahoton, matar ta Fatakwal, ta ce danyen mai tan 237,875 Yunin 2018, inda KRPC lta sarrafa 21,855 a Janirun 2018.
Bugu da kari, a bisa fashin bakin da NNPC na kudi na watan day a gabata da ayyukan dana rahoton ayyuka na Janairun 2019 ya nuna cewa, karfin iya aikin matatr ta Fatakwal daga Yulin 2018 zuwa Janirun 2019, kusan babu wani abin azo a gani, inda kuma na matatar KRPC, daga Fabirairun 2018 zuwa Janairun 2019 shima bau wani abin azo a gani da akayi.
Daga cikin matatun man kasar nan guda uku da kamfanin NNPC yake kula dasu, matar Warri ce kacal take sarrafa danyen mai daga Janairu 2018 zuwa Janairun 2019.
Wakilinmu ya lura da cewa, daga Janairun 2018 zuwa Janairun 2019, matatr man ta Warri bata yi wani katabus ba daga Satumba zuwa Okotobar 2018.
A cikin Janiru, matatar man ta Warri, ta sarrafa danyen mai 104,459, inda ya kai kashi 19.76 bisa dari.
A cikin Janairun 2019 ayyukan da matatun man KRPC, Fatakwal da kuma Warri, dukkan aikin su bai wuci kashi 5.5 bisa dari ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: