Connect with us

MAKALAR YAU

Uwa Mafi Karancin Shekaru A Duniya: Labarin ’Yar Shekara Biyar Din Da Ta Haihu

Published

on

A wannan makon zan dan shiga cikin harkar haihuwa ne, saboda a makon da ya gabata mun tattauna batun mutuwa. Sai dai wannan zagayen ba zan yi bayanin haihuwa kaitsaye ta fuskacin alakarta da karuwar al’umma ba ne. Akwai labari mai muhimmancin gaske wanda shi ne zai dauki kaso mai yawa na rubutun.
Kamar yadda na fadi a gabatarwan rubutuna makon da ya gabata cewa ita mutuwa a ko da yaushe ta na janyo raguwan al’umma ne, sannan kuma ita mutuwa babu wanda zai ce shi babu ruwanshi da ita, ko da babu ruwanka da ita, ita akwai ruwanta da kai. Kowanne mutum dole ne ya na da alaka da mutuwa.
Amma a al’amarin haihuwa kuwa, idan mutum ya ga dama babu ruwanshi da shiga sha’anin, saboda idan ka ga dama za ka iya kin yin aure, ko kuma ko da ma ka yi auren, sai ka dauki matakan hana samuwar haihuwa. Ka ga kenan, a bangaren haihuwa mutumya na da zabi biyu; ya haihu ko kar ya haihu. Wanda a al’amarin mutuwa babu wanda ke da wannan zabi, dole ne kawai a mutu.
A wasu lokutan ilmi na tabbatar da al’amarin da a ka shigar a kundi ne kawai. Kamar misali; za ka ga a na cewa wanda ya fi kowa dadewa a duniya shi ne dan shekaru 113, alhali ko kuma watakil a kauyenku ma akwai tsohuwar da ta kai shekaru 120. Saboda ita tsohuwar da ke zaune a kauyenku lokacin da a ka haife ta babu wani rijistar haihuwa, wanda rashin wannan rijistar zai haifar da shakku gaa adadin shekarun da za ta fadi.
Idan Allah ya nufa, nan gaba kadan zan yi nazarin labarin matar da ta fi duk wata Mace yawan haihuwa a duniya, wata Mata ‘yar kasar Rasha, wacce ta haifi ‘ya ‘ya 69. Ka ga wannan labarin ya zama an amshe shi ne, saboda matakan da a ka bi wurin samunshi da tabbatar da sahihancin shi.
Haka kuma idan na ce ga labarin wata yarinya wacce ba a taba samun irinta a duniya ba; wacce ta haihu alhali shekarunta biyar da wata bakwai, ka ga zai yi wahala a samu wani wanda zai ce ai akwai wata, saboda wacce binciken musamman ya tabbatar ita ce dai wacce na ke magana. Idan kuma a ka samu wata a kauyenku ko garinku wacce ta haihuwa ta na shekaru 5 da wata shida shi kenan, ka ga an samu sabon ilmi da kuma sabon bayani kenan wanda ya shafe wanda a ke da shi a kasa.
A shekarun baya a 1939, wata ‘yar karamar yarinya mai suna Lina Medina ta haifi jariri mai rai da lafiya, alhali shekarunta na haihuwa biyar da watanni bakwai. Wannan labara ya girgiza duniya, ya girgiza masana wadanda su ka tafi a kan cewa mace na fara al’ada ne daga shekara 15 zuwa 49.
Kamar yadda ya ke a ilmance, mace na iya daukan ciki (juna biyu) ne a lokacin da ta shiga shekarun da zai yiwu ta fara jinin al’ada, wanda a ke kira da ‘Menarche’ shi ne bincike ya tabbatar da shekara 15 a ke farawa, wannan na iya zama akwai bambanci a tsakanin kasashe. Sannan kuma wannan jini na al’ada na tsayawa a yayin da mace ta kai shekaru 49 ‘Menopause’ shi ma wannan akwai bambancin shekarun tsayawa a kasashe, saboda akwai matan da ke daukan ciki a shekaru 50 ko 51.
Dalilin da ya sa na kawo wannan misalin shi ne don a fahimci irin karya lagon binciken kimiyya da labarin yarinya Lina Medina ya yi; ba ma a shekaru 10 ko tar aba, a shekara biyar na yarinta ta dauki ciki, wanda hakan ke nuna ashe ta fara jinin al’ada ne tun a cikarta shekara biyar a duniya, ta haihu bayan wata bakwai.
Lina Medina ‘yar wani kauye ne da a ke kira Ticrapo da ke kasar Peru. A yayin da iyayenta su ka lura cikinta ya yi tulele, sai su ka yi zaton ko wani nau’in ciwo ne ya taru a cikinta wanda hakan ya sa su ka yi gaggawan kai ta garin Pisco domin a duba ta; bayan dogon binciken da likitoci su ka yi ne su ka tabbatar da cewa Lina na dauke da juna biyu na wata bakwai. Dakta Gerardo Lozada ne ya amshi haihuwanta kuma shi ne ya fara tabbatar da cewa yarinyar na da ciki.
Ganin haka ne fa a ka shiga yiwa iyayenta tambayoyin da a ke son jin amsoshinsu. Likita Gerardo a bincikensa ya gano cewa yarinya Lina ta fara jinin al’ada ne tun a watanni bakwai baya.
Wannan rikitaccen al’amari na bukatar gamsasshen bayani daga mahaifin Lina, wanda sanadiyyan haka ‘yan sanda su ka yi awon gaba da shi bisa zargin keta haddin diyarsa da kuma laifin fyade. Wanda dole ta sa daga baya a ka sake shi, saboda rashin bayyanannun hujjoji. An sanyawa jaririn suna Gerardo wanda nauyinsa ya kai kilo 2.7, wanda a kundin tantancewa ta zamo Uwa mafi karancin shekaru. Jaririn da ta haifa mai suna Gerardo ya yi tsawon kwana a duniya, wanda sai da ya kai shekaru 40 kafin nan ya mutu.
Jaririn da Lina ta haifa har ya mutu bai san wanene hakikanin mahaifinshi ba; shin Lina yayarshi ce (idan mahaifinta ne ke da cikin) ko kuma uwarshi? Lina Medina ta ki ta bayyana hakikanin yadda a ka yi ta samu ciki.
Likitoci sun yi iyaka kokarinsu wurin yin gwajin kwayoyin halitta domin tantancewa tsakanin mahaifin Lina da jaririn da ta haifa don samun tabbaci, amma hakan ya ci tura. Wannan labari ne ingantacce wanda ya afku, ba tatsuniya ba ne ko shaci–fadi.

Mu hadu mako mai zuwa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!