Connect with us

KASUWANCI

‘Yan Sanda Sun Cafke Wani Bisa Zargin Karkatar Da Man Dizil Na Miliyan N10.7

Published

on

‘Yan sanda a karkashin ofishin shugaban sun a kasa sun chafke Ayodeji Owoeye dan shekara 40 mai sayar da man fetur da gas da ya yi ikirarin shi Manaja ne a kamfanin sayar da mai.
Ayodeji Owoeye ya shiga hannu ne saboda zargin sa da akayi na karkatar da mayan motcin dakon mai biyu dake dauke da litocin man Dizil 53, 000 da aka kiyasta kudinsu ya kai sama da naira 10,700,000.
‘Yan sandan ofishin na shugaban ‘yan sanda sun samu nasarar cake wanda take zargin ne bayan samun bayanan sirri akan badakalar.
A na dai zargin Owoeye, ya gabatar da kansa ne a matsayin Manajan kamfanin man na LAGBUS, inda ya tuntubi wani mai suna Mista Omotayo da sunan cewa, zai kawo masa litocin man Dizil 20 da kudin su ya kai naira miliyan 4.5 a cikin watan Satumbar shekarar 2018, amma ya kasa biyansa, inda mai makon hakan ya dinga bugewa da bayar da uzorori iri-iri akan gaza biyan bashin.
An ruwaito cewa, akoda wane lokacin Omotayo ya tambayi Ayodeji Owoeye akan kudinsa, ya san irin karyar da zai gaya masa, inda ya kance yana kokarin hada bashi kuma ya kara hakuri nan bada jimawa ba zai biya shi bashin.
A cikin watan Fabirairun wannan shekarar, Ayodeji Owoeye ya kara kirawo Omotayo don kawo masa litocin man Dizil guda 33,000 akan kudi naira miliyan to 6.2, inda tun a wancan loakcin yaki biyan Omotayo bashin.
Ganin cewa, Ayodeji Owoeye yana kokarin kin biyan bashin ne ya sanya Omotayo ya rubuta takardar koke zuwa ga Shugaban ‘yan sanda na kasa Mohammed Abubakar Adamu ta hannun Kwamandan shirin through IRT na ofishin shugaban na y’yan sanda Abba Kyari.
Bayan da aka cafko Ayodeji Owoeye, an gano cewa, Ayodeji Owoeye shi ba Manaja bane a kamfanin na yana kawai yin mafni da habar kamfanin ne don ya damfari alumma.
A cikin takardar da ya yiwa ‘yan sanda bayani, wanda ake zargin ya amsa cewa, ya jima yana damfarar alumma ta hanyar yin amfani da harabar kamfanin LAGBUS don ya damfari alumma, inda yake fakewa cewa shi Manaja ne a kamfanin da ke kula da motocin bas na kamfanin don yin aiki a cikin gari.
A cewarsa, ” Kwarai tunda farko na tambayi wani ya kaiwa wani mai suna Joseph litocin man Dizil guda 20,000 bayan day a sheda mini cewa, yana bukatar man don sanyawa generate na kafar sadarwar yanar gizo akan kudi naira naira miliyan 4.5.”
Ya kara da cewa, “ Na jima ina yin wannan harkallar tare da Joseph, inda hakan ya kai kusan shekaru uku zuwa yanzu, amma nayi mamaki da hanr yanzu ya gaza biya na kuma duk loakcin dana kira layin wayarsa ta tafi da gidan ka, nakan ji a kashe.”
Ya cigaba da cewa,‘’Na kuma hadu da wani mai suna Mista Omotayo don kara kai masa litocin man Dizil 33, 000 da kudinsu ya kai naira miliayn 6.2, inda ya kara da cewa, a yanzu hakan da nake Magana da kai, bai biya ni ko kwabo ba, jimlar bashin da ya kamata in biya Mista Omotayo naira miliayn 10.5.”
A cewarsa,‘’Wannan laifi nane domin Omotayo bai san wani da ake kira Joseph ba, amma ban san cewa, Joseph zai yi hakan ba, matsalr ita ce, ban san inda zan ga Joseph ba don in tabbatar cewa, Joseph ya kai man na Dizil litoci 53,000 da kudinsa ya kai naira miliayn 10.7 domin nine Mista Omotayo ya sani a matsayin mai saye.”
Ya kara da cewa, ”Ni ne cikakken Manajan gudanar da aiki na kamfanin LAGBUS, amma an umarce ni da in kara gaba bayan da aka samu sababan mahukunta a kamfanin, inda hakan ya bani kwarin gwaiwar shiga harabar kamfanin na LAGBUS Ina son in tabbatar yanzu ba na aiki a kamfanin domin an sallame ni.”
A cewarsa, ‘’Sam ban san Mista Omotayo yaje kamfanin LAGBUS dake a Ojota, inda ya yi kamar har yanzu ya na yin aiki a kamfanin ba.”
“Wanda ake zargin, ya ganni ian fita daga kamfanin na LAGBUS, inda na dauka har yanzu yana yin aiki a kamfanin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: