Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Daure Matashi Na Tsawan Wata 12 Bisa Yi Wa Budurwarsa Sata

Published

on

Kotun Ejigbo ta daure wani matashi mai su na Chinedu Wisdom, na tsawan wata 12 a gidan yari, bisa samun sa da laifin satar kudi da kuma wasu kayayyaki mallakar  budurwarsa. A cewar lauya mai gabatar da kara, ASP Supol Kenneth Asibor, wanda a ke tuhuma  ya shiga shagon Esther Ginikanwa, da ke garejin Jakande cikin yankin Ejigbo, inda ta ke sayar da  jakunkuna. “Bayan ya kammala cinikin wasu kayayyaki, sai Wisdom ya bukaci soyayyan daga wajen  yarinyar, inda ya bayyana mata  cewa, ya auri wata ‘yar kasar Indiya,sai dai ta mutu a makon da ta gabata, shi dai fasto ne, sannan kuma shi likita ne. “Bayan ya nuna ma ta makulin motarsa, ya bukaci ta rufe shagonta, inda ya nemi ya kai ta gidansu da  ke yankin Ijegun, ita kuma ta yarda  su ka  je gidansu,” in ji shi.

Asibor ya kara da cewa, bayan sun kammala cin abinci tare da Ginikanwa a gidansu, sun gudanar da soyayya, inda ta kai har su ka kwana  tare a cikin gidansu. Ya ce,  tana tashi da safe, sai ta gano cewa, ya sace mata  tsabar kudi har naira 150,000, wayar salula da kuma wasu kayayyaki wanda kudin su ya kai na naira 15,000. An gurfanar da wanda a ke zargin a gaban alkali mai sharia’a T.  O. Shomade, inda ya same shi da laifin da a ke tuhumar sa da shi, kuma ya yanke masa hukuncin zama a gidan yari na tsawan wata 12.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!