Connect with us

LABARAI

An Fara Taro Kan Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Na Kasashen Afrika

Published

on

A yau talata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci bude taron yaki da cin hanci da rashawa na kasashen Afirka. Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a dakile amfani da kudaden sata wajen tafiyar da harkokin siyasa da kuma zabe.

Shugabannin kasashen Afirka da suka halarci taron sun hada da shugaba Buhari na Nijeriya, da Paul Kagame na Rwanda da takwarorinsu na Ghana da Liberia da Senegal.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi yayin taron akwai shugaban kasar Rwanda Paul Kagame, wanda zai yi magana kan sahihin zabe, matsalar baiwa masu kada kuri’a cin hanci da kuma yadda za a magance matsalar ta cin hanci da ta fadada a tsakanin al’umma.

Tsohon shugaban hukumar zaben Nijeriya Farfesa Attahiru Jega kuwa, jawabinsa ya mayar da da hankali ne kan rage barna ta da kudade kan gudanar da zabe, da kuma amfani da kudi kan masu kada kuri’a, sai kuma nauyin da ya rataya a wuyan hukumomin tsaro, wajen tabbatar da doka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!