Connect with us

WASANNI

Bale Zai Je Zaman Aro Na Shekara Biyu A Manchester United

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana son daukar dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale, a matsayin aro na tsawon shekaru biyu sakamakon zaman rashin tabbas da yakeyi a kasar Sipaniya.

Tun bayan komawar mai koyarwa Zinadine Zidane kungiyar dai ya gayawa Bale cewa baya cikin tsarinsa kuma bazaiyi amfani dashi ba wanda hakan yasa dan wasan ya shiga halin rashin tabbas sai dai ya bayyana cewa yanason cigaba da zaman kungiyar a haka duk da bazai dinga buga wasa ba.

Sai dai duk da haka abune mai wahala dan wasan ya zauna tsawon shekaru uku baya buga wasa a kungiyar wanda hakan yasa ake ganin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United zata dauki aron dan wasan domin ya koma kasar Ingila da buga wasa.

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana daga kasar Ingila, kungiyar kwallon kafa ta Manchester United tana shirin daukar aron dan wasan nan da wasu kwanaki domin ya cigaba da buga wasa a kungiyar.

Wasu rahotannin kuma sun tabbatar da cewa Manchester United tanason daukar aron dan wasan na tsawon shekaru biyu kuma zata dinga biyan gaba daya albashinsa irin wanda yake karba a Real Madrid kuma ana ganin dan wasan zai amince da hakan.

Manchester United dai tana tsoron siyan dan wasan domin ya zauna din-din-din a kungiyar sakamakon yayi fama da ciwo a shekaru biyu da suka gabata kuma tana ganin idan ta siyeshi zai sake komawa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!