Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Batun “Tsaron Kasar Amurka” Ya Kasance Kamar Wani Kwando Da Ake Iya Sanya Kome A Ciki

Published

on

Kama daga kayayyakin karafa, da karfen goran ruwa, ko motoci, ko na’urorinsu na gyara da ake shigar da su Amurka, ko masana’antu masu jarin waje, ko zuba jari kai tsaye, sannan ko dalibai da masana na ketare, har ma yanzu ana neman duk wanda yake neman izinin shiga kasar Amurka ya bayar da dukkan bayanai na akantarsa dake shafukan sada zumunta, kusan kome da kome, yanzu a ganin gwamnatin Amurka, dukkansu suna kawo barzana ga “tsaron kasar Amurka”. A idon bangaren Amurka, batun “tsaron kasa”, wato wani batu ne mai tsanani sosai ga kowace kasa, tamkar dai wani kwando ne da ake iya sanya kome a ciki.
A ganin galibin kasashen duniya, batun “tsaron kasa” shi ne hali maras hadari da ba a kai wa wata kasa barzana a fannonin ikon gwamanti, da ikon mulkin kasa, da dinkuwar cikakken yankunan kasa, da fatan alheri na al’umma, da dauwamammen ci gaban tattalin arziki, da zamantakewar al’umma, da sauran fannonin dake da alaka da muhimmiyar moriyar kasar.
A hakika dai, batun yana kunshe da hakikanin abubuwa a bayyane sosai. Amma yanzu, kasar Amurka, wato kasa mafi karfi a duk duniya, tana amfani da shi kamar yadda take so, har ma ya kasance kamar wani kayan aiki da take amfani da shi a lokacin da take aiwatar da manufofin ba da kariya ga cinikayya, domin tabbatar da ikonta na babakere.
Bisa kididdigar da aka yi, an ce, daga shekaru 80 na karnin da ya gabata zuwa farkon karni na 21, kasar Amurka ta taba kaddamar da bincike bisa “sharadi na 232” har sau 14, amma daga karshe dai, ta dauki matakin sanya takunkumi ga matsaloli 2 ne kawai daga cikinsu. Wannan ya bayyana cewa, a da, ba a kullum ake ganin kasar Amurka tana daukar matakan kakaba takunkumi kan cinikayya bisa hujjar “tsaron kasa” ba.
Amma, tun daga shekarar 2017, Amurka ta ji tsoro sosai saboda fargabar tsaro, hakan ya sa ta mayar da kayayyakin karafa da karfen goran ruwa, kashin motocin da take shigowa da su daga ketare, da kuma jarin ketare, ’yan ketare, kana da kamfanonin masu jarin ketare, da kimiyya da fasahohin ketare na zamani, da dai sauransu, a matsayin kalubaloli ne ga tsaron kasar, har ta yi bincike bisa “sharadi na 232” sau da dama. A sanadin haka kuma, ta sanar da shiga halin ko ta kwana a watan Mayu na bana, matakin da ya tsorantar da jama’arta kwarai da gaske. Kuma ta kawo illa ga kawarta da abokan cinikinta, har suka yi mamaki sosai: a matsayin kasa mafiya karfi a fannin karfin soja, kimiyya da tattalin arziki, wane ne ke da karfin haifar mata da wata illa a fannin tsaro?
Kowa zai iya ba da amsa: ba wanda zai iya kawo barzana ga tsaron kasar Amurka. Hakika dai tunanin Amurka na yin gaban kanta, da kuma yin babakare na kokarin dakile abokan cinikinta don kiyaye moriyar kai a karkashin hujja “tsaron kasar”. Abin da ya bayyana cewa, Amurka ba ta iya tinkari sauye-sauyen duniya, wadanda ba a taba ganin irinsu cikin karnin nan ba, kuma ba za ta iya fuskantar tasowar sabbin kasuwanni da bunkasuwar kasashe maso tasowa ba, har ta ji tsoro kan bunkasuwar tattalin arzikin da ci gaban kimiyar sauran kasashe. Har ma ta dauki wasu matakai na rashin imani, bisa hujjan “tsaron kasa”. Wannan hujja dai ta zama matakin da Amurka ta kan dauka yadda ta ga dama.

Dangane da batun, gwamayyar kasa da kasa sun fahimci gaskiyar lamarin. Ga misali, kungiyar tarayyar kasashen Turai EU ta ce, kasar Amurka ta kan fake da “barazana ga tsaron kasa” don neman daukar matakan kare wasu sana’o’in cikin gidanta. A nasu bangare, hadaddiyar kungiyar sarrafa kayayyakin karafa ta kasa da kasa ta kasar Amurka, da wasu kamfanoni mambobin kungiyar guda 2, sun yi hadin gwiwa wajen kai kara ga kotun ciniki tsakanin kasa da kasa ta kasar Amurka, a bara, inda suka zargi ayar doka bisa sharadi na 232, wanda a bisa ayar ne gwamnatin kasar Amurka ta fara daukar matakan karbar karin haraji kan kayayyakin karafa da ake shigarwa cikin kasar, da sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Sa’an nan yayin da ake sauraron karar, wani alkali ya taba tambaya ga wakilan ma’aikatar shari’ar kasar cewa, “Ko akwai wani kayan da ba za a iya karbar karin haraji kansa ba bisa dalilin tabbatar da tsaron kasa? Misali ko shugaban kasa zai iya kaddamar da karbar karin haraji kan miyar gyada?”
Hakika yadda kasar Amurka ta fi son yin amfani da kalmar “tsaron kasa” ya haddasa matsaloli ga abokanta a fannin ciniki, gami da raunana tsarin ciniki na kasa da kasa, da bata imanin da aka taba samu tsakaninsu. Har ma ya haifar da illoli ga kasar Amurka ita kanta.
Batun nan ya yi kamar wani labarin da aka bayyana cikin tsohon kundin labarai na “Aesop’s Fables”, wanda ya shafi wani yaro mai kiwon tumaki da kuma wani karkeci: Bayan da yaron ya yaudari mutanen kauyensa har sau da dama, bisa karyar cewa karkeci ya kai hari ga tumakinsa, to, daga bisani ko da yake wani karkeci na gaske ya farwa tumaki na sa, mutane ba za su ba da taimako ba, domin a ganinsu kamar kullum yaron ya yin ihun karya ne kawai.
Yanzu kasar Amurka tana ta amfani da kalmar “tsaron kasa”, to, idan ta saba da wannan dabara, ba za ta mayar da martani yadda ake bukata ga wata barazana ta gaske ba. Hakan, a hakika, shi ma barazana ce mafi girma da kasar ke fuskanta a fannin tsaro. (Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Amina Xu, Bello Wang, ma’aikatan CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: