Connect with us

WASANNI

Crystal Palace Ta Yi Fatali Da Tayin Manchester United A Kan Bissaka

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun tabbatar da cewa kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace dake kasar Ingila tayi fatali da tayin kudi fam miliyan 40 da Manchester United tayi domin siyan dan wasa Aaron Wan-Bissaka, dan kasar Ingila, mai shekaru 21 a duniya.

Manchester United dai tana kasuwa domin siyan dan wasan baya na gefen dama wanda zai maye mata gurbin Antonio Balencia, wanda yabar kungiyar yayinda kuma dan wasa Ashley Young baya kokari a wajen.

Sai dai Manchester United ta shiga neman dan wasa Wan-Bissaka wanda take ganin shine zaiyi mata maganin matsalarta bayan ya buga wasanni 39 a kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace a wannan kakar data gabata.

Sabon kociyan kungiyar ta Manchester United ne dai ya bayyana cewa zai siyi matasan ‘yan wasa domin gina sabuwar kungiya kuma yana son ya maye gurbin Antonio Balencia wanda yabar kungiyar a karshen kakar data gabata.

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace dai ta bayyana cewa ba ta son rabuwa da dan wasan mai shekara 21 a duniya sai dai tayin kudin da Manchester United zata yimata shine zaisa dole ta tsaya domin ayi ciniki kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Tuni Manchester United ta siyi dan wasa Daniel James daga kungiyar kwallon kafa ta Swansea City, dan kasar Wales wanda zai koma kungiyar da zarar an bude kasuwar siye da siyar da ‘yan wasa a gobe.

Manchester United dai zata fara buga wasannin sada zumunci da kungiyar kwallon kafa ta Perth Glory a ranar 13 ga wata mai kamawa sannan kwanaki hudu tsakani kuma ta buga wasan sa da zumunta da kungiyar kwallon kafa ta Leeds United a kasar Ingila.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!