Connect with us

KASUWANCI

Ghana Da Wasu Kasashe Sun Ayyana Sayen Man Fetur Daga Matatar Dangote

Published

on

Kafin kaddamar da matatar mai ta Dan gote, kasashen Afrika dake shigo da mai da kuma masu rabar da man dake kasar Ghana, suna bayyana zakuwar su ta sayen man fetur da daga matatar man ta Dangote in ta fara gudanar da aikin ta.
Masu sayen man, sun bayyana cewar, tuni sun gama shirye-shirye don shigo da man daga babba daya tilon matatar man dake a yankin Lekki cikin jihar Lagos mallakar sannanen dan kasauwar Alhaji Aliko Dangote.
Bayanin hakan yana kunshe ne a cikin takardar da Kamfanin rikunonin Dangote ya gabatar a ranar litinin a taron masu harkar mai na kasa da kasa na (Ghipcon) da aka gudanar a shekarar 2018, wanda ya gudana a Accra babban birnin a kasar Ghana.
Sanarwar ta kara da cewar, mahalarta taron da kuma masu rabar da man da sauran ‘yan kasuwa da suka fito daga kasashe da ban-da-ban sun kagara su san yadda zasu shiga sahun rabar da man daga ganguna 650,000 daga matatar.
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya sanar da cewar, gwamnatin kasar Ghana ta sanar da cewar, tafi son ta yi hudda da matatar man ta Dangote wajen shigo da man mai makon shigo dashi daga kasuwar duniya.
Ya kara da cewa, “ya fi ma na sauki mu sayi man daga matatar mai ta Dangote saboda tafi mana kusa da sauran kasashen da muke makwabtaka dasu.”
Nana Akufo-Addo wanda mataimakin sa Mahamud Bawumia ya wakilce shi a wurin taron yaci gaba da cewa, kasashen Afrika sun kagara matatar man ta Dangote ta fara aiki.
A cewar Mista Babajide Soyode, wani mai bayar da shawara akan a kamfanin na Dangote da kuma harkar mai, ya sanar da cewar, a lokacin da mataimakin shugaban kasar da ministan makamashi na kasar Boakye Agyarko, suka kai ziyara a matatar man ta Dangote, sunyi mamaki sosai yadda suka ga aikin inda kuma suka nuna gamsuwar su akan yadda aikin yake tafiya kamar yadda ya dace.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!