Connect with us

RAHOTANNI

Kwankwaso Ne Ya Fara Bincikar Sarki Sanusi Ba Ganduje, Cewar Hamza Darma

Published

on

An bayyana cewa, jagoran Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ne ya fara bincikar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II kan wasu zarge-zarge a lokacin da ya ke mulkion jihar. Don haka ba gwamna mai ci, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ne farau wajen tuhumar sarkin ba.
Wannan bayanin ya fito a wata tattaunwa da wakilin LEADERSHIP A YAU ya yi da dattijon jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Hamza Usman Darma, inda ya bayyana cewa tabbas ba Gwamna Ganduje ne ya fara ja wa sarkin kunne ba, kamar yadda wasu ke ta faman kumfar baki a kai.
“Sa-toka-sa-katsin da ke tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da Gwamna Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ba wata ‘yar manuniya ce da ke bayyana wasu abubuwa na Sarkin Muhammadu Sanusi II, da ba a sani a baya ba,” in ji shi.
Darma ya bada tarihin cewa, “Kamar dai yadda aka sani Tsohon Gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ne ya kawo Muhammadu Sunusi II, kan karagar kujerar Sarautar Kano, wanda ga duk wanda ke birnin Kano ya san yadda jama’ar Kanon su ka shiga dimuwa sakamakon jin sunan Sanusi Lamido Sanusi, kafin ya koma Muhammadu Sanusi II.
“Bayan rasuwar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, jama’ar Kano duk sun gamsu da cewa, ko shakka babu guda daga cikin ‘ya’yan marigayin za a nada ya gaji mahaifinsu, amma kwatsam, sai tsohon gwamna na wancan lokaci ya sanar da sunan Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin na Kano.
“Hakan ya ta da hankalin daukacin al’ummar Jihar Kano, da ya sa har aka yi k zaton akwai yiwuwar barkewar rikici a cikin jihar, amma saboda kyakkyawar tarbiya irin ta Kanawa suka karbi wannan al’amari duk da cewa, ba shi al’ummar Kanon ke so ba.”
Ya ci gaba da cewa, daga lokacin da gwamnan wancan lokacin, Rabiu Musa Kwankwaso ya ambata Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano, sai da Sarkin ya kwashe tsawon kwanaki uku a gidan Gwamnatin Kano ba tare da ya iya fitowa waje ba domin gudun tunzurin al’umma. Amma daga bisani aka raka shi Fadar Kanon cikin tsauraran matakan tsaro da ka iya cewa, al’ummar Jihar ta Kano sun jima ba suga irinsa ba, kuma haka Sarkin ya ci gaba da shimfida mulki kamar yadda kowa ya ganewa idonsa.
Duk da waccan gudunmawa da Kwankwaso ya baiwa Muhammadu Sanusi II, sakamakon wani tsari da shi kadai ya san abin da yake nufi, sai da Gwamna Kwankwaso ya ba shi takardar Jan kunne har sau biyu. Takarda ta farko, an ba shi ne lokacin da Gwamnatin Kwankwaso ta tsara kokarin magance matsalar barace-barace a fadin Jihar Kano, ta inda har doka aka samar a kai, amma Sarki Muhammadu Sanusi II, ya ci gaba da tara almajiarai a kofar Fadarsa yana ba su sadaka.
Gwamnatin, ta ja hankalinsa a kan wannan al’amari, amma ya toshe kunnuwansa. Wannan burus da Sarkin ya yi ne ya sa Gwamna Kwankwaso ya ba shi takardar jan kunne a karo na farko. Takardar Jan Kunne na biyu kuma ta biyo bayan karya ka’idar da duk wani ma’aikaci ya sani ne cewa, idan jami’i ko wani ma’aikaci zai fita wata kasa bisa doka dolene sai ya nemi izinin Shugabansa, kamar yadda tsarin yake a kan shi kansa Sarkin. Ma’ana dai a duk lokacin da Sarkin ya shi yin tafiya wajibi ne ya sanar da gwamnan tare da neman izni kafin ya tafi, amma Sarkin ya ki yin biyayya ga wannan tsari na tsohuwar gwamnatin, in ji shi.
Haka nan, a wancan lokaci ko da Sarkin ya rubuta takardar yin tafiyar tasa, to fa ba wai ta neman izni ba ce, illa kawai ta sanarwa, kuma tun kafin takardar ta kai ga zuwa gaban gwamna ma, tuni ya yi ficewarsa. Wannan ta sa Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, ya kara dankara masa wata takardar jan kunnen a karo na biyu. Saboda haka, bisa abubuwan da ke faruwa a Kano a yau, ba wani sabon al’mari ba ne, ko shi wanda ya yi wa Sarkin dukkanin wani karamci (Kwankwaso), sai da ta kai ga ya kai shi ga bangon da tasa dole ya ba shi takardar jan kunne har karo biyu.
Har ila yau, wannan dalili ne ya sa wasu Masana ke kallon Gwamna Ganduje, a matsayin Damo Sarkin Hakuri. Sannan idan aka dubi takardar sakamakon binciken da Hukumar sauraren korafe-korafen Jihar Kano ta fitar, ta tabbatar da yadda Sarkin ya tsinci kansa a inda ba a taba zato ba. Duk da dai cewa, a cikin takardar amsar jan kunnen da gwamnatin Kano ta baiwa Sarki sanusin, ta bayyana cewa Sarkin ba shi da wata alaka ta kai tsaye da asusun ajiyar Masarautar ta Kano, amma dai abubuwan da suka bayyana a cikin rahoton Hukumar ya haska fitilar wata badakala mai nauyin gaske, musamman ma yadda rahoton ya nuna kashe kudi har sama da Naira Milyan 54, a kan sayen Datar yanar gizo na Kamfanin Airtel, a cewarsa.
Haka kuma, rahoton Hukumar sauraron korafe-korafen ya koka da salon
zagon kasar da Sarkin ke yi mata ta hanyar hana wadanda aka gayyata kimanin su hudu don bayar da karin wasu muhimman bayanai a cikin
tuhume-tuhumen da ake yi wa Masarautar, inda mutun guda ne kadai daga cikin su ya mutunta gayyatar Hukumar Isa Bayero, ya kuma halarci Hukumar tare amsa tambayoyin da aka nema daga wurinsa, sannan har yanzu yana ci gaba da taimakawa wannan Hukuma.
Haka zalika, wasu na ta bayyana cewa, an samu sulhu tsakanin Gwamna Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi, a ganawar da suka yi a babban birnin tarayya Abuja, sai dai Sakataren yada labaran Gwamnan Malam Abba Anwar, a gefe guda ya musunta hakan, inda ya bayyana cewa babu wani batun sulhu a tsakaninsu illa iyaka, an fara tattaunawa za kuma a ci gaba da mutunta juna.
Amma kamar yadda aka sani ne Masarautar ta Kano ta gurfanar da Gwmnatin Kanon a gaban Kotu, kuma ana ci gaba da sauraren karar a halin yanzu. Haka ita ma, Hukumar sauraron korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa, na ci gaba da gudanar da nata aikin, a cewar Dattijon.
Bugu da kari, abin da ake bukatar jama’a su fahimta a nan shi ne, Gwamna Ganduje da Sarki Muhammadu Sanusi II, sun gana a Abuja kuma za a ci gaba da mutunta juna, amma batun sauran Masarautu guda hudu na nan daram suna ci gaba da karbar mubaya’a a kulli yaumin ta Allah, in ji Darma.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!