Connect with us

LABARAI

Majalisa Ta Tara: PDP Ta Bukaci Membobinta Su Zabi Sanata Ndume Da Bago

Published

on

Jam’iyyar PDP ta bukaci membobinta da su zabi Sanata Ali Ndume da Umar Bago a matsayin shugaban majalisar Dattawa ta tara da kuma Kakakin majalisar. PDP ta cimma wannan matsayar ne bayan zaman tattaunawa da ya gudana a tsakanin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar wanda ya hada da shugabannin jam’iyyar, gwamnonin jihohi, da kuma Sanatoci da ‘yan majalisunta wadanda aka zaba a karkashin jam’iyyar.

Zaman tattaunawar ya gudana ne a gidan gwamnatin jihar Bayelsa da ke birnin tarayya Abuja a jiya Litinin. Inda a karshen zaman Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Umar Ibrahim Tsauri ya fitar da sanarwar goyon bayansu ga takarar Sanata Ndume da kuma dan majalisa Umar Bago.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!