Connect with us

RIGAR 'YANCI

Matar Suntai Ta Sake Musulunta, Ta Auri Dan Uwan Turai Yar’Adua

Published

on

Uwargidan marigayi tsohon gwamnan jihar Taraba Hauwa Danbaba Suntai ta daura aure da dan uwan Uwargidan Shugaban kasa Marigayi Umaru Musa Yar’Adua, wato Hajiya Turai Ya’Adua, a karshen makon da ya gabata.

Hauwa Suntai ta daura aure da Sa’ad Malami, haifaffen Katsina kuma hamshakin dan kasuwa biyo bayan ta amshi addinin Musulunci, inda a ka daura auren a babban masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja.

Hajiya Hauwa ‘yar asalin jihar Borno da ma tunda farko Musulma ce, sai dai ta koma addinin Kirista ne bayan da ta auri gwamnan jihar Taraba, Marigayi Danbaba Suntai, fiye da shekaru 20 kenan.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa, Sa’ad Malami dan shekaru 30 dan uwa ga Turai Yar’Adua, ya amince ya auri Hauwa Danbaba Suntai ‘yar shekaru 50 ne biyo bayan musuluntar da ta yi.

Tsohon mijin Hauwa Danbaba Suntai dai ya samu mummunan raunuka a jiki da kwakwalwa ne a wani hadarin jirgin saman da ya yi cikin watan Disambar 2012, ya kuma mutu a ranar 28 ga Yuni, 2017, a garin Houston cikin jihar Florida da ke kasar Amurka.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!