Connect with us

MANYAN LABARAI

Matashin Dan Shekara 32 Ya Zama Shugaban Majalisar Jihar Oyo

Published

on

‘Yan majaljsar jihar Oyo sun zabi wani matashin dan siyasa mai shekara 32, Adebo Ogundoyin dake wakiltar mazabar Ibarapa ta gabas ta jihar Oyo a matsayin sabon kakakin majalisar dokoki jihar ta tara, ba tare da wata hamayya ba.
Ogundoyin ya zama dan majalisa a shekara ta 2018 bayan mutuwar tsohon kakakin majalisar Michael Adeyemo. Olagunju Ojo wanda ya fito daga mazabar Oriire dake Ogbomoso ya maye gurbin Adeyemo bayan mutuwar sa, rahotanni sun bayyana cewa Adebo ya dare wannan mukami ne bayan samun amincewa da kuma goyon bayan kafatanin ‘ya’yan majalisar dokokin su 32, sakamakon amfani da wasu ma’aunai da yan majalisar suka yi wajen zaben shugabansu.
Daga cikin ma’aunan da yan majalisar suka duba wajen zabo Adebo akwai jam’iyyarsa ta PDP, lura da tsarin karba karba, da kuma kasancewarsa guda daga cikin yan majalisu guda hudu da suka sake komawa majalisar bayan lashe zabe a zaben 2019. Daga cikin wadanda suka halarci zaman zaben shuwagabannin majalisar akwai sabon gwamnan jahar Oyo, Seyi Makinde, da mataimakinsa Rauf Olaniyan, da kuma sauran jiga jigan sabuwar gwamnatin jihar Oyo
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!