Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Mutum Biyar Sun Rasa Rayukansu A Hatsarin Mota A Hanyar Abuja

Published

on

Mutum biyar ciki har da ma’urata sun rasa rayukansu, a wani hatsari wanda ya afku a babban hanyar Abuja ranar Asabar. Mutum 6 kuma sun samu mummunar raunika, a wannan hatsari wanda ya faru da misalin karfe 8 na safe, kusa da mahadar Setraco da ke kan babban hanyar Kubwa, an dai garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asitti.

A cewar jami’an hukumar kiyaye hadarruka, Mista Emmanuel Agbo, hatsarin ya faru ne lokacin da wata mota kirar Toyota Camry, wacce ta fito daga garin Abuja ta bugi tirela. Agbo ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a wurin da lamarin ya faru cewa, hatsari ya shafi fasijoji 6 da ke cikin motar, inda lamari ya janyo cinkoso ababan hawa.

“Lamarin ya tilasta wa motar mai lamba kamar haka ABC 978 SL, bugun gefan gadar da ke babban hanyar. “Mutum biyar daga motar ciki har da wasu ma’aurata sun mutu nan take. Ga gawar su nan a kasa. “An garzaya da mutum 6 wadanda su ka samu raunika zuwa asibiti.   

“Mu na kokarin kwashe gawarwakin zuwa dakin ijiye gawarwaki da ke asibitin gari,” in ji Agbor.

Ya kara da cewa, tirelan ba ta tsaya ba lokacin da ta bugi motar, amma duk da haka, sai da ‘yan sanda su ka cafke dareban tirelan.

Jami’in dan sanda mai suna, Danjuma Garba, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya faruwar lamarin, sannan ya bayyana cewa, an samu nasarar cafke direban tirelan. A cewarsa, lokacin da direban tirelan ya gudu, sai mu ka sanar wa dukkanin jami’anmu, inda a ka samu nasarar cafke direban tirelan a garin Aya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!