Connect with us

WASANNI

Ranar Alhamis Real Madrid Za Ta Gabatar Da Hazard Gaban Magoya Bayanta A Santiago

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid za ta gabatar da sabon dan wasan da ta siyo daga Chelsea, Eden Hazard a gaban magoya bayanta ranar Alhamis bayan da Madrid din ta dauko Hazard daga Chelsea kan yarjejeniyar shekara biyar, kan kudi da ake cewa zai kai fam miliyan 150.

Kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Portugal ya koma Chelsea daga Lille a shekara ta 2012, ya kuma bar chelsea ne bayan da ya lashe manyan kofuna shida da buga wasa 352 ya kuma ci kwallaye 352.

Hazard ya buga wa Chelsea wasa na karshe da kungiyar ta doke Arsenal a Baku da ci 4-1 ta lashe Europa League, inda ya ci kwallo biyu ya kuma taimaka aka ci daya a karawar wadda kuma  aranar ya bayyana cewa ba zai sake bugawa kungiyar wasa ba.

Kawo yanzu Real ta dauki ‘yan kwallo biyu kenan har da dan wasan Frankfurt mai ci wa kungiyar kwallaye Luka Jobic wanda aka biya fam miliyan 52 sai dai daman tun ana tsaka da kakar wasa kungiyar ta siyi dan wasan baya na FC Porto, Elder Militao dan kasar Brazil.

Real Madrid ta kasa taka rawar gani a kakar da aka kammala, inda Ajad ta yi waje da ita a gasar cin kofin zakarun turai wadda ita ke rike da kofin haka kuma Barcelona ce ta lashe kofin La Liga na bana, yayin da Real ta kare a mataki na uku, kuma Barcelona ce ta fitar da Real a gasar Copa del Rey na kakar da ta wuce.

Kawo yanzu kuma Real Madrid tana zawarcin dan wasan tsakiya inda take son siyan dan tsakiyar Manchester United, Paul Pogba ko kuma na Tottenham, Cristian Eriksen, dan kasar Denmark kuma har ila yau kungiyar ta kusa siyan dan wasan baya na Lyon, Ferland Mendy, dan kasar Faransa.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!