Connect with us

WASANNI

Ronaldo Ya Tambaye Ni Ko Zan Koma Juventus, Cewar De Ligt

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Ajad Amsterdam, dan kasar Holland, Matthijs De Ligt, ya bayyana cewa shahararren dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Jubentus, Cristiano Ronaldo ya tambayeshi ko zai iya komawa Jubentus domin su buga wasa tare a kakar wasa mai zuwa.

De Ligt mai shekara 19 a duniya yana daya daga cikin matasan ‘yan wasan da tauraruwarsu take haskawa a wannan lokaci kuma kungiyoyi da dama ne da suka hada da Barcelona da Jubentus da PSG da Manchester United suke zawarcinsa.

Sai dai Ronaldo ya bayyana karara cewa yanason ya buga wasa da De Ligt a Jubentus inda ya tambayi dan wasan ko zai iya komawa kungiyar duk da cewa akwai manya manyan kungiyoyin da suke zawarcin dan wasan.

An hango Ronaldo ya na magana da De Ligt bayan an tashi daga wasan da Portugal tazama zakara a gasar cin kofin Nations League da suka buga da Holland a daren ranar Lahadi bayan da dan wasa Guedes ya zurawa Portugal kwallonta daya wadda ta bata nasara.

“Ronaldo ya tambayeni ko zan koma Jubentus amma da farko ban fahimci abinda yake nufi ba saboda hankalina yana kan tunanin yadda mukayi rashin nasara a wasan karshe domin idan kayi rashin nasara hankalinka yana gushewa” in ji De Ligt

De Ligt dai ya taimakawa kungiyarsa ta Ajad ta lashe gasar rukuni rukuni ta kasar Holland sannan kuma ya taimakawa kungiyar taje wasan kusa dana karshe na cin kofin zakarun turai inda Tottenham ta dokesu sai dai a hanya sune suka doke kungiyoyin Real Madrid da Jubentus.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: