Connect with us

KASUWANCI

Shirin Gina Gidajen Najeriya: Kamfanin China Zai Zuba Jarin Dala Miliyan 300

Published

on

Kamfanin da a ke kira ‘One Belt One Road’ na kasar China ya sanar da cewar ta hanyar kamfanin, gwamnatin kasar ta China, zata zuba jari na dala miliyan 300 a shirin gina gidaje masu yawa na Nijeriya nan bada jimawa ba.
Daraktan kamfanin, Mista Steben Kim ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da kamfanin.da ake kira Zbecan Homes Estates ya shirya. a garin Abuja.
Mista Kim yace, kamfanin nasa na One Belt One Road tare da hadin gwaiwar kamfanin Zbecan Homes and Estate wanda a kwanan baya suka rattaba hannun yarjejeniya ta fahimta zasu gina gidaje guda 5000 a Abuja da kiwayen ta.
A cewarsa, zuba jarin zai kamfanin nasa damar cimma burin manufar kafa kamfanin da aka yi a kasar China, inda ya kara da cewar, manufar.itace, don a taimaka wajen gudanar da ayyukan da mutane zasu amfana.
Ya ci gaba da cewa, “mun fito ne daga kamfanin da ake kira One Belt and One Road dake kasar China kuma kamfanin da ya zuba jari akan ayyukan.da kai tsaye, suka shafi rayukan alummar dake cikin nahiyar Afrika kuma munzo nan ne don baiwa kamfanin da ake kira Zbecan akan ayyukan su, musamman na shirin hukumar gina gidaje na ma’aikatan gwamnatin tarayya (FISH).”
Mista Kim ya kara da cewa, “munyi amanna cewar, wannan aikin zai amfani rayuwar alummar garin Abuja da kuma Nijeriya baki daya kuma zamu iya zuba kudi akan aikin ta hanyar ofishinmu.”
Ya sanar da cewar, zuba jarin ba kawai zai kasance a na kudi bane harda sanya kayan wutarlantarki da na’ura mai aiki da hasken rana da sauran su.
Shi ma a nashi jawabin, Manajin Darkta na kamfaninin Global Hint Construction na kasar China daya daga cikin kamfanonin da za’a yi amfani dasu, Mista Aigbe Osagie yace, irin wannan ayyukan tuni, ana kan ci gaba da aiwatar dasu a kasashen Kenya da kuma Angola.
A cewarsa, tuni sun gina sama da gidaje 5000 a kasashen Angola da Kenya, kuma su na son gina makamantan hakan a Nijeriya.
Mista Osagie ya yi nuni da cewar, kalubalen da ake fuskanta wajen yingini a nahiyar Afrika ita ce ta yanayin kasar yin gini, inda ya kara da cewa, amma kasar yin gini irin ta China tafi kyau a bisa ta.kasashen dake Afrika.
Nicholas Ogbede, Manajin Darakta na kamfanin Zbecan Homes Estate ya sanar da cewar, jarin da gwamnatin China zata zuba, zai taimaka wajen kawar da kalubalen da ma’aikata suke fuskanta na gidajen kwana.
A cewarsa, a bisa kimiyyar da China take dashi da ban-da-ban wajen aikin gini zata taimaka wajen samar da ragi na tsadar gini wajen gina gidaje ga ma’aikatan gwamnati ‘yan Nijeriya.
Ya sanar da cewar, kamfanin Zbecan Homes Estate ya kuma rattaba hannu ta yarjejeniyar fahimta da ofishin shugabar ma’aita ta tarayya don gina gidaje 700 a karkashin shirin gwamnatin tarayya mai suna FISH.
A cewarsa,“muna son mu samar da gidaje masu saukin kudi a wurare masu kyau ga ma’aikata ganin cewar, mafi yawanci suna yo tattaki daga wurare maso nisan gaske zuwa gun aiki a kullun.
Ya sanar da cewar, “a yanzu hakan muna da sama da 5000 da suka nuna suna bukatar gidajen mu kuma mun yanke shawarar yin amfani da shirin gidauniyar gina gidaje na kasa (NHF) don samar da gidaje ga ma’aikata.
A cewarsa, “muna kuma kan yin kokari wajen tuntbar ma’aikatu da sassa da kuma hukumomi da za su samar da kaya don yin gine-gien mu akan farashi mai sauki don mu cimma burin da muka sanya a gaba.
Idan za a iya tunawa, ‘yan kasar na China masu gina gidajen, a cikin watan Afirilun shekarar 2018 ce, suka kawo ziyara Nijeriya don gudanar da bincike da kuma auna kasa dangane da guraren da zasu yi gina gidajen.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!