Connect with us

RIGAR 'YANCI

Shugabancin Majalisar Dokoki: Gwamnonin APC Sun Goyi Bayan Takarar Lawan Da Gbajabiamila

Published

on

Gwamnonin jam’iyyar APC sun goyi bayan takaran Sanata Ahmad Lawan da kuma Femi Gbajiamila, a matsayin shugaban majalsar Dattawa da kuma Kakakin majalisar wakilai ta kasa, a zaman da majalisar za ta yi a zango na Tara, wanda aka kaddamar da zaman nata a yau din nan. sabon shugaban kungiyar gwamnonin na jam’iyyar APC da aka zaba, Gwamnan Jihar Kebbi, Atiku Bagudu ne ya shaidawa manema labarai hakan a jiya da dare, ya ce gwamnonin sun mika goyon bayansu ga zabin da shugaba Buhari ya yi ba tare da wata tantama ba.

Bagudu ya ce, za su yi duk mai yiwuwa na ganin Lawan da Gbajiamila sun yi nasara.

Ya ce, kan gwamnonin ya hadu a kan goyawa matsayin da jam’iyyar ta dauka baya, suka kuma umurci dukkanin zababbun Sanatoci da su ma su goyi bayan wannan matsayin. Bagudu ya ce, “Mun yi amfani da wannan damar inda muka tattauna a kan hakan, inda muka mika wuya ga shawarar da uwar jam’iyyarmu ta zartas a kan batun shugabancin majalisun na tarayya. A koda-yaushe, gwamnonin jam’iyyar APC sun kasance masu yin biyayya ne ga duk shawarar da uwar jam’iyyar su, Shugaba Buhari suka dauka domin ganin dai an cimma manufa.

“Domin ganin hakan, dukkanin mu baki-daya mun goyi bayan takaran Sanata Ahmed Lawan, a matsayin shugaban majalisar Dattawa, da kuma Honorabul Femi Gbajiamila, a matsayin Kakakin majalisar wakilai ta kasa, dukkanin gwamnoni kuma sun aminta da wannan zabin, za kuma su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar na su. Dangane kuma da wasu wakilan jam’iyyar ta APC da suke nuna rashin amintar su da yanda jam’iyyar ta yi rabon mukaman, sai ya ce, “Muna umurtan Sanatocinmu da wakilanmu a majalisar wakilai ta kasa da su goyi bayan matsayar da jam’iyyar ta dauka, abin da karfafa gwiwa ganin yanda sauran jam’iyyu suke farin ciki da matsayar da jam’iyyarmu ta dauka na baki-daya ba tare da wani korafi ba.”

Taron Gwamnonin dai ya sami halartar Gwamnonin Jihohin, Edo, Lagos, Kano, Neja, Nasarawa, Kogi, Filato, Gombe, Osun, Ekiti, Kwara, da kuma mataimakan Gwamnonin Jihohin Kaduna da Borno.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!