Connect with us

LABARAI

Shuwagabanni Kadai Ke Da Tabbacin Tsaro Yanzu A Hanyoyin Najeriya – Gwamnan Ondo

Published

on

Gwmanan Ondo, Oluwarotimi Akeredolu ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane kan hanya, to sai dai ya tabbatar da cewar za a kawo karshen lamarin ba da nisa ba.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wani shirin da ya yi da gidan rediyo ranar Lahadi a garin Akure babban birnin jihar.

Gwamna Akeredolu ya koka da cewar, babbar hanyar Akure zuwa Ibadan ta kazanta da ma su garkuwa da mutane, inda ya bayyana cewa, ko a ‘yan kwanakin baya sai da jerin gwanon motocinsa ya yi ta kan wasu da a ke zargi da ‘yan garkuwar ne kafin su ka gudu zuwa cikin daji.

Gwamnan ya ce, yanzu manyan mutane ma su tawagar jami’an tsaro kamar gwamna, mataimakin gwamna ne kadai ke da tabbacin iya bin hanya ba tare da faruwar wani abu ba.

Da ya ke bada labari, gwamnan ya ce, kadan ya yi saura da an farmaki tawagarsa in banda harbin da jami’an tsaron da ke masa rakiya su ka yi a sama, abunda ya tsoratar da maharan su ka tsere zuwa daji.

Gwamnan ya kara da cewa, ba kamar manyan mutane ba da ke samun rakiyar jami’an tsaro ba, abun ya fi shafuwar talakkawa da ke tafiya tsirara ba tare da jami’an tsaro ba. Ya tabbatar da cewa, matafiya a hanyar ba sa da tabbas.

Da ya ke wasa da dariya, gwmanan ya ce, “yanzu na fi karfin wani ya yi garkuwa da ni.”
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: