Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Hali Mara Tabbas

Published

on

Bisa kididdigar da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta bayar a Litinin din nan, an ce, a cikin farkon watanni 5 na bana, jimillar kudin cinikayya da kasar Sin ta yi ta kai kudin Sin RMB yuan triliyan 12.1, wato ta karu da 4.1% bisa kwatankwacin lokacin bara. A waje daya, a cikin gajeren hutu na kwanaki 3 da aka kammala jiya, yawan masu bude ido na cikin gidan kasar Sin ya karu da 7.7%, yawan kudin da aka kashe a wajen yawon bude ido a cikin wadannan kwanaki 3 ma ya karu da 8.6%.
Yanzu, takaddamar cinikayya da ake yi a tsakanin kasa da kasa tana ta tsananta, saurin karuwar cinikayya tsakanin kasa da kasa ma ya ragu sosai, amma cinikayyar da kasar Sin ta yi da sauran kasashen duniya tana ta samun karuwa, yawan kudin da aka kashe a lokacin hutu ma ya karu sosai. Wannan ya alamta cewa, har yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana da karfi sosai, kuma zai iya samun karin ci gaba nan gaba. Tattalin arzikin kasar Sin da ya kasance kamar wani teku zai iya fama da kowane irin hadari.
Abin da aka fi mai da hankali shi ne, cinikayyar kasa da kasa da kasar Sin ta yi a cikin farkon watanni 5 na bana tana da halaye musamman guda biyu.
Da farko dai, yawan kayayyakin yau da kullum da kasar Sin ta fitar ko shigar da su ya karu da 6.1%. Yawan kudin cinikayyarsu da aka yi ya karu da 1.1% bisa jimillar kudin cinikayya da kasar Sin ta yi. Wannan ya bayyana cewa, aikin kyautata tsarin sana’o’in kasar Sin yana taka rawa kamar yadda ake fata, karfin gogayyarsu ya samu karfafu a kasuwannin kasa da kasa.

A hannu guda kuwa, duk da cewa adadin kudi shafar cinikayya tsakanin Sin da Amurka ya ragu da kashi 9.6 cikin dari a farkon watanni 5 na bana, wanda ya kai kashi 11.7 cikin dari bisa na dukkanin adadin ciniki tsakanin Sin da kasashen ketare, amma wannan adadi ya ci gaba da karuwa a wasu muhimman kasuwani ciki hadda EU, ASEAN da Japan da dai sauransu. Ban da wannan kuma, saurin bunkasuwar cinikayyar shige da fice tsakaninta da kasashe da shawarar “Ziri daya da hanya dake” ke shafa ya fi saurin bunkasuwar irin wannan cinikayya tsakaninta da kasashen ketare sauri na kashi 4.9 cikin dari. Matakin da ya alamta cewa, Sin ta kara samun abokiyar cinikayya masu dimbin yawa, Sin na da karfi tinkari kalubale ta fuskar cinikayyar shige da fice ta hanyar daidaita tsarin kasuwannin kasa da kasa.
Adadin cinikayyar shige da fice na farkon watannin 5 ya fi yadda aka yi hasashe, duk da ganin Amurka ta kara tsananta takaddamar ciniki tsakaninta da kasar Sin. Tattalin arzikin kasar Sin zai tafiya yadda ya kamata saboda yana da tushe mai inganci, duk da ganin wasu kalubale da aka kawo masa.
A hakika dai, Sin ta sha tinkarar da wawuyacin hali a baya, alal misali rikicin hada-hadar kudi a nahiyar Asiya na shekarar 1997, da kuma irin wannan rikici na kasa da kasa na shekarar 2008, hakan ta koyi darasi sosai daga wajensu har ta kara karfi da dabarunta. Sin kasa ce dake kan matsayin biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kuma kasa ce mafi karfi a fannin masana’antu, kana kuma kasa ce dake da yawan kudaden ajiyar cikin gidan kasar, kuma yawan GDPn kasar ya kai RMB yuan triliyan 90, ban da wannan kuma tana da kasuwa mai yawan mutane biliyan 1.4 da tsarin masan’antu a fannoni daban-daban mai kyau, abin da ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin na da inganci sosai wajen tinkarar kome kalubaloli da wahalhalu a gabanta.
Duk da haka, yanzu kasar Sin ta daina mai da cikakken hankali kan yawan tattalin arziki da saurin karuwarsa, yayin da neman ci gaba mai inganci ya zama batun da ya fi janyo hankalin kasar. A halin yanzu, bakatun cikin gida ya samar da gudunmawa ga karuwar tattalin arzikin kasar Sin da ta kai fiye da kashi 100%, ta yadda wannan bangare ya taka rawa mafi muhimmanci a kokarin ciyar da tattalin arzikin kasar gaba. A sa’i daya kuma, yadda tattalin arzikin kasar ke dogaro kan ciniki da kasashen waje ya ragu zuwa kimanin kashi 33%, hakan ya nuna tsarin tattalin arzikin na kara inganta.
Tun bayan da kasar Sin ta zama daya daga cikin mambobin Kungiyar Ciniki ta Duniya (WTO) wasu shekaru 18 da suka wuce, kasar ta taka muhimmiyar rawa a kokarin dukule kasashen duniyarmu a waje guda, tare da samun damar raya kanta. Ban da haka, ta samar da dimbin damammakin zuba jari, da ciniki, gami da guraben aikin yi ga sauran kasashe.
Bayan da kasar ta gabatar da shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya”, ta kara kokari wajen nuna ma duniya niyyarta ta neman amfani juna da cin moriya tare, da kwarewarta a wannan fanni, gami da takamaiman matakan da ta dauka don cika alkawarinta. Daga shekarar 2013 har zuwa ta 2018, kasar Sin ta yi ciniki da kasashen da suka halarci shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” sosai, inda yawan kudin cinikin ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 6000, yayin da kamfanonin kasar Sin suka zuba ma wadannan kasashe jarin da ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 90.
Tattalin arzikin kasar Sin, wanda ke ci gaba lami lafiya duk da matsalolin da ake fuskanta a duniya, ya zame ma tattalin arzikin duniya wani abun dake kwantar da hankalin kowa. Idan an yi nazari kan alkaluman tattalin arzikin duniya a shekarun baya, za a gano cewa kasar Sin ta samar da kashi 30% na karuwar tattalin arzikin duk duniya. Saboda haka, tsohon firaministan kasar Faransa, Jean-Pierre Raffarin, ya taba bayyana cewa, “yadda kasar Sin ke kasancewa cikin wani yanayi na tabbas wajen samun ci gabanta wani abu ne mai daraja sosai, wanda da kyar a ke samusa a wannan zamanin da mu ke ciki.”
Sa’an nan bisa hasashen da kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki OECD ta yi, kasar Sin za ta ci gaba da samar da mafi yawan gudunmowa ga karuwar GDP din duniya.

(Masu Fassarawa: Sanusi Chen, Amina Xu, Bello Wang, ma’aikatan CRI Hausa)
Advertisement
Click to comment

labarai

%d bloggers like this: