Connect with us

RIGAR 'YANCI

Wasu Na Kokarin Kawo Wa APC Rudani A Jihar Bauchi, In Ji Matasan APC

Published

on

Majalisar Matasan jam’iyyar APC a karkashin lemar ‘APC Youth Parliament, reshen jihar Bauchi’ sun ce, akwai yunkurin da wasu ke yi a jihar Bauchi domin wargaza zaman lafiya da kwanciyar hankalin jam’iyyar APC a jihar, suna masu shaida hakan da cewar munakisa ne da aka kintsa don kawo hargitsi.

A wani taron manema labaru da suka kira a karshen mako a sakatariyar ‘yan jaridu da ke Bauchi, shugaban kungiyar Kabiru Garba Kobi da sakataren kungiyar Malam Nasiru Cigari, sun karanta takardarsu da take dauke da zargin da suke yi na cewar akwai hanun jam’iyar PDP da ke mulki a jihar wajen kawo APC rashin zaman lafiya.

Suke cewa; “Sun leka sun gano cewar APC jam’iyyar adawa ce a jihar, amma karfinta da yawan ‘yan majalisun jihar da take da su babban barazana ne ga jam’iyya mai mulki, don haka ne suka dauka wa kansu aikin wargaza zaman lafiya da kawo rudani a cikin jam’iyyar APC a jihar domin cimma wasu manufofinsu,”   

“Duba da ababen da suke faruwa wanda wasu ke shiga gidajen rediyo suna fade-faden maganganun da za su iya kawo wa APC rudani da rashin jituwa, muna ganin da bukatar a kawo karshen wannan matsalar ta hanyar gano cewar akwai masu tunanin zabe a 2023 tun yanzu,” A cewar Nasiru Cigari.

Cigari ya kara da cewa, akwai zarge-zargen tafiyar da jam’iyyar da ba daidai ba da ake yi kan shugaban jam’iyyar APC a jihar wato Uba Ahmad Nana, yana mai fadin hakan ma a matsayin wani shiri ne kawai na masu kafar angulu, “A kundin tsarin da jam’iyyar APC idan har shugaban jam’iyyar na jihar Bauchi ya take wani doka ko karya wasu ka’idoji da har wasu ke ganin ya karya doka, akwai hanyoyin da dokar jam’iyyar ta shimfida a sashi na 13 da sakin layin A-B da kuma sashi 21 da karamin sashi na 1-2-3-4  da za a bi domin hukuntawa ko tantance laifi aka yi ko ba laifi ba,” A cewar kungiyar.

Don haka ne kungiyar ta dada jaddada goyon bayanta ga jagorancin  Uba Ahmad Nana domin sun gamsu da salon mulkinsa “kuma babu wani laifi da ya bayyana  a kansa kawo yanzu. Don haka muna kimarsa tana nan daram,”

“Muna son uwar jam’iyyar APC na kasa da ta yi watsi da dukkanin wani bayanin da jita-jitan da za a kai mata na tsegumi, balla zaman lafiya da ci gaban jam’iyyar wasu ke son yi a matakin jihar, don haka muna fatan uwar jam’iyyar za ta watsar da aniyar masu son kawo rudanin. Muna da imanin jam’iyyar PDP da ke mulki a jihar ta tabbatar APC babbar barazanace a gareta don haka ne wasu ke neman yadda za su balla zaman lafiyar jam’iyyar domin su samu sarari,” A cewar kungiyar.

Wakilinmu ya tuntubi Kakakin jam’iyyar PDP na jihar Bauchi Yayanuwa Zaimabari domin jin batu kan zargin shisshigi da matasan APC ta ce PDP na musu, amma hakarmu bai cimma ruwa ba, kana bai amsa kirar wayar da muka masa ba lokacin da muke hada rahoton.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!