Connect with us

Nahiyar Afirka

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 100 A Mali

Published

on

Akalla mutum 100 ne aka kashe a wani mummunan hari da wasu mahara suka kai wani kauye a tsakiyar kasar Mali, a harin baya bayan nan da ya addabi yankin. Ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan hari, amma kisan dimbim jama’ar da aka yi a garin na al’ummar Dogon ta yi kama da ramuwar gayya.

Wannan harin na zuwa ne kasa da watanni uku bayan wasu mahara da ake zargi ‘yan al’ummar Dogon ne da ba a san ko su waye ba, sun halaka akalla mutum 160, ‘yan kabilar Fulani a wani kauye.

Jami’ai a gundumar Koundou, inda kauyen Sobane – Kou yake, sun ce an samu gawarwaki 95 a kone, kuma suna ci gaba da neman saura 19 da suka bace, haka kuma an yanke dabbobi da dama, sannan aka cinna wa gidaje wuta.

Kamfanin dillancin labaran Fransa ta ce ta ji wata majiyar tsaro a Malin na cewa an shafe ilahirin al’ummar wani kauyen Dogon daga doron kasa.

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!