Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Cafke ‘Yan Ta’adda 100 A Jihar Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sandar Jihar Kano ta gurfanar da sama da mutum 100 wadanda a ke zargi da aikata laifukan ta’addanci wadanda su ka safi garkuwa da mutane, kisan kai, fashi da makami, shan muyagun kwayoyi da kuma mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.  Da ya ke bayar da rahoto a shalwatan ‘yan sanda da ke garin Bompai, kwamuishinan ‘yan sandar jihar, Mista Ahmed Iliyasu, ya bayyana cewa, “rundunarsa ta kaddamar da farmaki a lokacin bikin sallah  da kuma bayan sallah, inda ta samu nasarar cafke sama da mutum 90 wadanda a ke zargi a ranr 30 ga watan Mayu da kuma ranar 7 ga watan Yuni.”

Iliyasu ya ce, an kai farmaki a kan masu garkuwa da mutane, wanda ya yi sanadiyyar cafke mutum uku wadanda a ke zargin masu garkuwa da mutane ne, Abdullahi Ali, Sani Rabe da kuma  Shuaibu Idi, wadanda su ka addabi jihohin Katsina, Zamfara da kuma Jihar  Kano. Ya kara da cewa, “su na gudanar da ayyukansu ne a Jihar Kano, a kananan hukumomin da su ka hada da  Gwarzo, Kiru, Bebeji, Shanono, Rogo, Karaye, da kuma Madobi da ke cikin garin Kano.”

Ya cigaba da cewa, wadanda a ke zargin sun bayyana cewa, su na da bindiga kirar AK47 har guda  biyar, wanda wani mutum mai su na Gemu ya ke boye musa a dajin Zamfara, ‘yan sanda sun kaddamar da farautar mutumin. Kwamishinan ‘yan sandar ya ce, “lokacin da su ka kai farmaki a ranar hudu da kuma ranar biyar ga watan Yunin shekarar 2019, an samu nasarar cafke mutum 90 wadanda a ke zargi a yakunan    Gan, Dawakin Kudu, Ungogo, Dala, karamar hukumar Kano ta tsakiya, ciki har da rukunin gidaje na Bachirawa Kuarters, Pan-Shekara, Kwanar Hudu, Dakata da kuma rukunin jidaje na Zangon-Dakata Kuarters.”

Ya ce, an kwato jakar wiwi guda 14, wuka guda 64, almakashi, gatari, layoyi da kuma muyagun kwaya daga hannun wadanda a ke zargi. Ya kara da cewa, za a gurfanar da wadanda a ke zargin a kotu, idan a ka kammala bincike.

A cewarsa, “a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 2019, tawagar ‘yan sanda sun gudanar da sintiri a kan titin Independent da ke Dakata cikin garin Kano, an samu nasarar cafke Abba Abubakar  dan asalin Jihar Borno da kuma Sumaila Hassan da ke rukunin gidaje na Dakata Kuarters, inda a ka cafke su da  bindiga kirar gida. Ana gudanar da bincike,  domin a gano manufar su.”

Ya ce, an samu nasarar cafke ‘yan ta’adda guda 12 a rukunin gidajan Sani Mainagge Kuarters, inda su ke yi wa fasinjoji raunika.. ya kara da cewa, an kwato tulin wiwi, dogayen wuka  guda uku, kananan wuka guda hudu, adduna guda biyu da kuma layoyi da dama. Ya cigaba da cewa, za a gurfanar da wadanda a ke zargi a kotu, idan a ka kammala bincike. Ya na mai cewa, an cafke barayin Babura guda biyu tare da wasu mutum biyar wadanda su ke hada kai su na ta’addanci, sannan ‘yan sanda sun samu nasarar cafke wani mutum mai suna Abdullahi Musa, barawon motoci.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!