Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

’Yan Sanda Sun Kashe Kasurgumin Dan Ta’adda A Jihar Ribas

Published

on

A jiya ne rundunar ‘yan sandar Jihar Ribas ta bayyana cewa, ta samu nasarar hallaka kasurgumin dan ta’adda mai suna ThankGod Nwandiko wanda a ke yi wa lakabi da kwamandar Buky. Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Musa Belel, shi ya bayyana hakan a garin Fatakwal lokacin da ya ke gurfanar da wani dan ta’adda wanda su ka cafke a kwanakin nan a jihar. Ya bayyana cewa, an cafke dan ta’addan ne a yankin Omarelu cikin karamar hukumar Ikwerre, bayan samun bayanan sirri, an kashe shi ne a yankin Isiokpo lokacin da ya yi yunkurin gudu daga hannun tawagar ‘yan sanda.

Kwamishinan ya siffanta Nwandiko a matsayin kasurgumin mai garkuwa da mutane, dan fashi da makami, mai kisan kai, sannan kuma dan kungiyar asiri wanda ya addabi yankunan Omerelu da Owerri.

‘Yan sanda sun gurfanar da wani direban banki mai suna Chris Kani, wanda a ke zargin ya na bai wa ‘yan fashi da masu garkuwa bayanai a kan abokan kasuwancin banki da kuma bayanai game da amsar kudin fansa daga banki. Ya amsa cewa, ya su na shirin yin garkuwa da managan bankin tare da shugaban masu tallace-tallace na bankin, amma sai ya canza ra’ayinsa, inda ya bayyana wa abokanansa cewa managan bankin ya yi tafiya zuwa kasar ketare.

Kwamishinan ya kara da cewa, lolacin da su ka samu bayanan sirri, nan take su ka tura jami’an ‘yan sanda, inda su ka fasa rumbun makamansu tare da cafke Israel Amadi dan shekara 41 da kuma Michael Okunna mai shekaru 35. “An samu nasarar cafke su ne ranar 16 ga watan Mayu, a kan hanyar Elele Alimini cikin karamar hukumar Emohua. An kwato tsabar kudi har naira 889,000 daga hannunsu.

“Haka kuma, ‘yan sanda karkashin jagorancin Jobinus Iwu sun gurfanar da wasu gungun  masu garkuwa da mutane da  fashi da makami, masu shekaru 19 da kuma 31. An samu nasarar cafke su ne a sassa daban-daban na cikin jihar. An cikin makaman da a ka kwato daga wajen su sun hada da bindigar AK-47 guda uku, harsasai guda 25, bindigogi kirar gida, motoci guda hudu, kayan sojoji da dai sauransu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!