Connect with us

LABARAI

Yau Za A Zabi Shugabannin Majalisa Ta Tara

Published

on

A yau za a kaddamar da majalisar dokoki ta tara a Nijeriya, inda za a zabi sabbin shugabannin da ake sa ran za su yi aiki tare da bangarorin zartarwa da na shari’a domin ciyar da kasar gaba. Sai dai rahotanni na nuna cewar, an samu rarrabuwar kawuna kan wadanda ake bukatar ganin sun samu shugabancin Majalisun biyu duk da cewa, Jam’iyyar APC mai mulki ke da rinjaye a tsakanin ‘yan Majalisun.

A yayin da APC ta bayyana goyan bayanta ga Sanata Ahmed Lawal da Femi Gbajabiamila a matsayin wadanda take so, Jam’iyyar PDP ta hannun Sakatarenta na kasa Umar Tsauri ta ce, tana goyan bayan Sanata Ali Ndume da Hon. Umar Bago domin shugabancin Majalisar.

Jam’iyyun na APC da PDP sun yi wata ganawa a tsakaninsu a jiya Litinin, inda suka tattauna kan sabuwar Majalisar da za a kaddamar a yau.

Da dama daga cikin al’ummar Nijeriya sun koka kan yadda aka yi ta samun rashin jituwa tsakanin shugabannin Majalisar da bangaren zartarwa a wa’adin farko na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, lamarin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin abubuwan da suka haifar da tsaiko wajen gudanar da ayyukan ci gaba a kasar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!