Connect with us

KASASHEN WAJE

An Fara Zanga-zangar Adawa A Birnin Hong Kong

Published

on

Dubban Mutane ne a yau Laraba suka sake gudanar da zanga zangar adawa da shirin amincewa da wata doka da za ta bada damar tasa keyar wanda ake zargi da aikata laifuka daga Hong Kong zuwa Sin domin yi masa shari’a. Masu zanga zangar akasarin su matasa da dalibai ne, inda suka yiwa ofisoshin gwamnati kawanya, suka hana motoci motsawa domin ganin Majalisa ta yi watsi da dokar.

Ganin yadda tururuwar masu zanga-zangar ta mamaye jami’an tsaron da suke cikin damarar ko ta kwana, shugabannin Majalisa sun bayyana dakatar da muhawara kan dokar zuwa wani lokaci nan gaba.

A shekara ta 2017 aka zabi Carrie Lam a matsayin sabuwar shugaba Hong Kong bayan kwamitin da ke goyon bayan Sin sun kada kuri’ar. Zaben dai a lokacin ya fuskanci suka daga ‘yan kasar da suke son a ba kowa yancin kada kuri’a, maimakon wasu tsiraru.

Tun kafin kada kuri’a kamar dai yadda masu sharhi suka yi la’akari aka yi hasashen Carrie Lam mataimakiya ga shugaban Hong Kong da Sin ke ra’ayi za a zaba. Kwamitin zaben ya kunshi membobi 1,194, kuma Lam ta lashe zaben ne da yawan kuri’u 777.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: