Connect with us

WASANNI

An Samu Rashin Jituwa Tsakanin Zidane Da Perez Kan Vinicious

Published

on

Wasu rahotanni daga kasar Sipaniya sun bayyana cewa an samu rashin fahimtar juna tsakanin mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinadine Zidane da shugaban gudanarwar kungiyar Florentino Perez akan matashin dan wasa Vinicious Jr.

Dan wasan mai shekara 18 a duniya ya zura kwallaye bakwai a raga sannan ya taimaka an zura guda 13 cikin wasanni 36 da ya bugawa kungiyar, wanda hakan ya sa ya zama babban matashin dan wasan da kungiyar ta ke ji da shi.

Kamar yadda rahotannin su ka tabbatar kociyan kungiyar Zidane ya na son kungiyar ta bayar da aron Vinicious, domin ya je wata kungiyar a kakar wasa mai zuwa, domin ya sake samun gogewa, yayin da shi kuma Perez ya ke ganin gwanda a bari yaron ya samu gogewa a kungiyar.

Dan wasan dai ya na daya daga cikin ‘yan wasan da su ka buga wasanni da dama a kungiyar a kakar wasan da ta gabata, inda ya ke samun damar buga wasa duk da cewa ‘yan wasa irinsu Isco da Bale da Asensio ba sa samun damar buga wasa.

Har ila yau zuwan Edin Hazard kungiyar zai rage wa dan wasan damar buga wasanni masu yawa kamar na kakar wasan da ta gabata.

Akwai bukatar a samu hadin kai tsakanin Perez da Zidane. Idan kuwa ba su warware matsalar ba, a kan dan wasan matsalar za ta kare, domin Zidane ne mai saka ’yan wasa su buga kwallo.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!