Connect with us

WASANNI

An Yi Rikici A Wasan Kano Pillars A Legas

Published

on

An samu wani rikici a wasan da aka kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Rangers a gasar zaratan kungiyoyi shida da ke taka leda a firimiyar Nijeriya da ake gudanarwa a birnin Legas. Rahotanni sun ce, magoya bayan Kano Pillars sun kai hari kan hukumomin da ke kula da gasar bayan kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki 1-1 a ranar Litinin.

Pillars ce ta fara jefa kwallon farko a minti na 59 ta hannun kaftin dinta Rabiu Ali, sai dai a daidai lokacin da ake gab da tashi wasan, Rangers ta farke ta hanyar bugun fanaritin da ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya.

Bayan tashi wasan ne, Rabiu Ali ya tunkari alkalin wasan cikin fushi domin nuna rashin jin dadinsa da tsawaita lokaci a zagaye na biyu na wasan da aka yi a garin Agege.

Hakan ne yasa magoya bayan Pillars su ma suka fantsama cikin filin wasan tare da jefe-jefen duwatsu da wasu karikitai. Sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kwashe hukumomin da ke kula da wannan gasa ba tare da yi musu lahani ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!