Connect with us

LABARAI

Asibitin Mahaukata Na Kware Ya Shirya Bitar Koyi-ka-koyar

Published

on

Asibitin kula da masu tabin hankali na gwamnatin tarayya dake Kware a jihar Sokoto ya shirya taron bitar koyi ka koyar ga kwamitocin lura da asibitoci na jihar Jigawa a garin Yakasawa dake Karamar hukumar Ringim

A jawabinsa jagoran tawagar likitocin Dr Muktar Gadanya yace an shirya taron ne domin fadakar da shugabannin kwamitocin hanyoyin da zasu bi wajen gano mutanen da suke da matsaloli da suka shafi kwakwalwa a cikin alumma.

Yace baya ga mahaukata da masu tabin hankali da kuma kwarkwar da kuma zararru akwai wadanda suke da cutar tabin kwakwalwa da basu sani ba.

Dr Muktar Gadanya ya kara da cewar an gudanar da irin wannan taron bitar a jihohin arewa maso yamma da suaksu ziyarci jihohin Kebbi da kuma Zamfara anan gaba

Yace taron bitar zai baiwa kwamitocin lura da asibitocin dammar taimakawa wajen bada shawara da kuma taimakawa wajen gano masu matsaloli da suka shafi kwakwalwa.

Alamun masu tabin hankalin sun hadar da yin tunani da yawan mantuwa da wasi wasi da sauransu

A nasa jawabin Dr Auwal Sani Salihu na sashen kula da masu tabin hankali na asibitin Mallam Aminu Kano yace an shirya bitar ne ga kwamitocin bisa laakari da kusancinsu ga jama-a wanda zasu iya taimakawa masu matsalar kwakwalwa a cikin alumma.

Yace sun fadakar tare da ilmantar da yan kwamitocin lura da asibitocin na Jigawa hanyoyin da zasu gano da kuma taimakawa masu matsalar tabin hankali tare da jan hankalin alumma kan illolin tsangwamar masu matsalar kwakwalwa

Daga bisani likitocin sun amsa tambayoyin mahalarta taron
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!