Connect with us

WASANNI

Ba Mu Ji Dadin Abinda Magoya Baya Su Ka Nuna Ba, Cewar Kano Pillars

Published

on

An samu hatsaniya a wasan da a ka kece raini tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars da Rangers International a gasar zaratan kungiyoyi shida da ke buga wasa a Firimiyar Najeriya da a ke gudanarwa a birnin Lagos.

Rahotanni sun ce, magoya bayan Kano Pillars sun kai hari kan hukumomin da ke kula da gasar bayan kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki 1-1 a ranar Litinin wasan da magoya bayan kungiyar da ‘yan wasan kungiyar su ka yi zargin ba a yi mu su daidai ba.

Kano Pillars ce ta fara jefa kwallon farko a minti na 59 ta hannun kyaftin dinta, Rabiu Ali, sai dai a daidai lokacin da a ke gab da tashi wasan, Rangers ta farke ta hanyar bugun fanaretin da ya haddasa tayar da jijiyoyin wuya.

Bayan tashi wasan ne, Rabiu Ali ya tunkari alkalin wasan cikin fushi domin nuna rashin jin dadinsa da tsawaita lokaci a zagaye na biyu na wasan da aka yi a garin Agege halin da masu sharhi akan wasanni sukayi fatali dashi.

Hakan ne yasa magoya bayan Kano Pillars su ma suka fantsama cikin filin wasan tare da jefe-jefen duwatsu da wasu karikitai sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar kwashe hukumomin da ke kula da wannan gasa ba tare da yi musu lahani ba.

Shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dai yayi Allah wadai da halin da magoya bayan kungiyar suka nuna inda kuma yace zai dauki matakin daya dace akan magoya bayan da suka nuna rashin da’ar.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!