Connect with us

Uncategorized

Burin APC Ya Cika: Lawan Da Gbajabiamila Sun Zama Shugabannin Majalisar Dokoki

Published

on

Bayan shekara hudu jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta na fafutukar ganin Sanata Ahmed Lawan daga jihar Yobe ta Arewa ya zama shugaban majalisar dattawan Najeriya, a yanzu wannan buri nata ya cika, inda mambobin majalisar su ka taru su ka zabe shi a matsayin sabon shugaban Majalisar Dattawa ta Tara a jiya Talata, 11 ga Yuni, 2019.

A takawarta kuwa, wato Majalisar Wakilai, nan ma dan takarar APC, Hon. Femi Gbajabiamila daga jihar Legas, ne ya lashe zaben, inda ya kayar da abokin karawarsa, Hon. Umar Bago daga jihar Neja.

Hon. Gbabiamila ya samu kuri’a 283, yayin da Hon. Bago ya samu kuri’a 76.

Shi kuwa Sanata Lawan ya doke abokin karawarsa, Sanata Ali Ndume daga jihar Borno,  ne, wanda ya sami kuri’u 28 kacal cikin kuri’u 107.

Ahmed Lawan, wanda shi ne kuma dan takarar da Shugaba Muhammadu Buhari ke goyawa baya, ya sami kuri’u 79, wanda hakan ya ba shi damar zama sabon zababben shugaban majalisar Dattawan Nijeriya.

Zaben, wanda a ka yi shi a wajen kaddamar da zaman majalisar na Zango na Tara, babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta goya wa abokin hamayyarsa Ali Ndume baya ne, amma duk da haka ya samu kuri’u 28, kamar yadda mu ka fada a baya.

Sanatocin da su ka halarci kaddamar da zaman majalisar dai su 107 ne, sanatoci biyu ne kacal da su ka fito daga Jihar Imo babu su a wajen a sakamakon takaddamar da ba a gama warware ta ba a kan zaben nasu.

Lawan, wanda har ila yau, shi ne dan takarar da jam’iyyar APC ke mara wa baya, Sanata Yahaya Abdullahi ne ya tsayar da shi, inda kuma Sanata Solomon Adeola Olamilekan, dukkaninsu daga jam’iyyar APC kuma daga Jihohin Kebbi da Legas, ya goyi bayansa.

Idan ba a manta ba, a shekara ta 2015 lokacin da za a kaddamar da Majalisa Ta Takwas, APC ta yi burin Sanata Lawan ya zama shugaban majalisar ne, amma hakan ba ta yiwu ba, inda Sanata Bukola Saraki, wanda yanzu ya fadi a zabe lokacin da ya sake tsaya wa takara a jiharsa lokacin manyan zabukan kasar a kwanakin baya, shi ne ya yi galabar zama shugaban a 2015.

An cigaba da turka-turka har majalisar ta kawo karshe, inda a yanzu APC ta fi yawan rinjayen da ya ba ta damar samar wa Lawan da yawan kuri’un da ya ke bukata, sabanin a 2015, inda PDP ta ke da tasiri sosai.

Shi ma Gbajabiamila, kamar Lawan, tun a 2015 APC ta so ya zama kakakin majalisar, amma hakarta ba ta cimma ruwa ba sai a yanzu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!