Connect with us

KASUWANCI

CBN Ya Zuba Karin Dala Miliyan 331.41 A Kasuwar Cinikin Hannun Jari

Published

on

A cigaba da kokarin samar da garanti a kasuwar musayar kudin musaya babban bankin Nijeriya (CBN) ya sayar da dala miliyan 331.41 ga masu hada-hadar kudi da ban-da ban don bayar da dauki don kare kasuwar daga durkushewa.

Bankin ya yi hakan ne a ranar juma’ar data gabata kuma Daraktan riko na sashen bayanai na bankin Isaac Okorafor ya tabbatar da hakan, inda yace, kamfanoni da suke sashen aikin noma da zirga-zirgar jiragen sama da kayan mai da sauran su, sune zasu amfana da daukin.

Okorafor yace CBN zai ci gaba da bayar da daukin a kasuwar don a kare ta daga durkushewa.Da yake kara jadda da tabbacin gwamnan bankin Godwin Emefiele, Okoro ya bayyana cewar, bankin yana da isassun kudi da zai tura zuwa kasuwar ta shinku don cimma burin samar da kudin musaya na kasashen waje a daukacin sassan kasuwar.

A cewarsa, dilolin da aka amince dasu, zasu iya samun kudin. Idan za a iya tunawa a ranar litinin data gabata ya kai ziyarar bazata ga wasu bankuna dake Abuja don ya tabbatar da cewar ana bin dokar da aka gindaya ta saye da sayarwar kudaden kasar waje na musaya da kuma sayarwa matafiya zuwa kasa shen duniya in har suna da takardu na hakika.

Bugu da kari, CBN a ranar laraba talatin ga watan Mayun 2018, ya zuba dala miliyan 100 ga dililin da aka amince dasu a sassan dake kasuwar kamar na matsakaitan masana’antu da kuma dala miliyan 55 da aka ware masu.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!