Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

Dalibin Jami’a Ya Shiga Hannu Bisa Zargin Sa Da Ayyukan Kungiyar Asiri

Published

on

Wani dalibin jami’ar Kalaba mai suna Ikezue Kingsley Nnadi, wanda ya ke karanata likitanci, masu gadin jami’ar Kalaba sun damke shi. An dai cafke wanda a ke zargin ne, bisa mallakar bindigoji.

Shugaban masu gadin jami’ar mai suna Jarlath Abang, shi ne ya gurfanar da wanda a ke zargin, ya bayyana cewa, an cafke shi ne a dakin kwanan dalibai da ke kan titin Moore, ta hannun wani mai gadi wanda ya ke kulawa da dakunan kwanan daliban. Abang ya kara da cewa, jami’an tsaron jami’an sun dade da samun bayanan asirri a kan ayyukan ‘yan kungiyar asiri a dakunan kwanan daliban, inda su ka dauki mataki wanda ya kai ga cafke wanda a ke zargin.

Shugaban ya ce, “Ikezue shi ne, shugaban ‘yan kungiyar asiri a dakunan kwanan daliban, kuma ya dade ya na guje wa masu gadin jami’an.”

Abang ya kara da cewa, wannan kame ba karamar nasara ba ce wajen dakile ayyukan ‘yan kungiyar asirin a cikin jami’ar. Shugaban jami’ar Farfesa Zana Akpagu ya samar da tsauraran dokoki game da ‘yan kungiyar asiri a jami’ar. Ya ce, “Masu gadin jami’ar  wadanda ke kulawa da dakin kwanan daliban, sun samu nasarar cafke wanda a ke zargin ne da misalin karfe biyu na dare. Amma kafin wannan kame, an dade ana jin karar harbe-harbe a dakunan kwanan daliban, wannan shi ya sa a ka dauki matakin gaggawa.”

Abang ya cigaba da cewa, an kwato karamar bindiga kirar gida, adduna, layoyi, muyagun kwayoyi, hudar ibilis, bajen kungiyar asiri na Aiye Confraternity da katuka da dama daga hannun wanda a ke zargin. Ya ce, za a gurfanar da wanda a ke zargin a wurin ‘yan sanda domin daukar matakin da ya dace.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!