Connect with us

LABARAI

DSS Ne Su Ka Ba Ni Cin Hancin Da Na Bai Wa Faruk Lawal, Cewar Otedola

Published

on

A ranar Litinin ce, Shugaban kamfanin mai na, Zenon Oil and Gas Limited, Femi Otedola, ya shaidawa babbar kotun birnin tarayya  da ke Apo, Abuja, cewa kudin nan dala dubu 620,000, da aka ga yana mikawa tsohon dan majalisar nan, Farouk Lawal, hukumar tsaro ta farin kaya DSS ne su ka ba shi su. otedola ya shaida hakan ne a lokacin da Lauyan Farouk Lawal, Mike Ozekhome (SAN), yake yi masa tambayoyin kwakwaf.

Ya kara da cewa, ya baiwa Farouk Lawan kudaden cin hancin da ake zargin ne a wani zama da suka yi. Ya ce, amma jami’an na DSS bas u kama Farouk Lawan hannu da hannu ba a lokacin da yake karban kudaden daga gare shi (Otedola), kamar yanda aka nuna a wani faifan bidiyo a cikin kotun.

Ya kuma shaidawa kotun cewa bas hi da wata shaida da za ta nuna cewa, jami’an hukumar ta DSS ne suka bas hi kudin , yana mai cewa ba a dunkule ne suka bas hi kudin ba, da kadan, da kadan ne suka bas hi su. ya kara da bayanin cewa, shi bai kuma rubuta lambobin da kudaden  da DSS din suka ba shi ba, ya kuma ce ba wata takarda da ya sanya hannu a kanta a lokacin da yake karban kudin daga gare su.

Da Lauyan ya tambaye shi, ko baya jin abin da ke cikin wannan enbelope din da aka nuna a cikin faifan bidiyon da ake mikawa Farouk Lawan din zai iya kasancewa wasika ce ko kuma katin gayyata ne.” Otedola wanda yake bayar da shaida a matsayin shaidar mai gabatar da kara na biyar ya ce, “Akwai yiwuwar abin da ke cikin enbelope din ya kasance wasika ce ko kuma katin gayyata.” Mai bayar da shaidan kuma ya shaidawa kotun cewa, a bisa la’akari da hotunan bidiyon, Farouk Lawan, bai cire hularsa yay i ta cika ta da dalolin ba.

Otedola y ace, Lawan wanda shi ne tsohon shugaban kwamitin majalisar wakilai ta kasa a kan tallafin mai, ya nemi a bas hi cin hancin dala milyan uku, wanda daga cikinsu ne aka far aba shi dala dubu 620,000. Ya shaidawa kotun cewa, ya san Phillip Akinola, wanda shi ne babban jami’in gudanarwa na kamfanin man na,  Zenon Oil and Gas Limited, amma bas hi da masaniyar cewa Akinola ya rubutawa Farouk Lawan wasikar sanar da shi cewa, kamfanin man na, Zenon, ya bayar da mai ga kamfanin main a, Forte Oil, a bisa wata yarjejeniya.

Wasikar dai, Ozekhome ne ya mikawa kotun ita a matsayin shaida, kotun kuma ta karbi wasikar a bayan da Lauyoyin suka yi ta musayar yawu mai tsanani. Bayan bayar da shaidar ta Otedola, Lauya mai gabatar da kara, Adegboyega Awomolo (SAN), ya shaidawa kotun cewa, masu gabatar da karan sun gama bayar da shaidunsu.

Mai shari’a Angela Otaluka, ta dage sauraron shari’ar har zuwa ranar 24 ga watan Satumba, 2019.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!