Connect with us

LABARAI

Ekweremadu Ya Dawo Da Motocin Gwamnati Da Ke Hannunsa

Published

on

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa a zaman majalisar da ya kare na Takwas a kwanan nan, Ike Ekweramadu, ya maido da dukkanin motocin gwamnati da ke hannunsa.

Wakilinmu da ya ziyarci wajen ajyar motocin mataimakin shugaban majalisar a safiyar Talata, ya tabbatar da dukknain motocin suna nan a wajen.

Wakilin namu ya lura da cewa, har ya zuwa ranar Litinin, Ekweramadu ne kadai cikin tsaffin shugabanin majalisar da har ya zuwa ranar bai maido da motocin na shi ba tukunna. Sai dai, wata majiya ta kusa da tsohon mataimakin shugaban majalisar ta shaidawa wakilin namu cewa, an dawo da motocin ne bayan da aka kamala yi masu garambawul da kuma wanke su tas a daren ranar ta Litinin.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!

%d bloggers like this: