Connect with us

MANYAN LABARAI

Gwamnan Zamfara Ya Gana Da Shugaban Miyetti Allah

Published

on

A yau Laraba Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya gana da shugabannin kungiyar fulani makiyaya wadda aka fi sani da Miyetti Allah, a kokarin shi na ganin an kawo karshen sata da yin garkuwa da mutane a jihar; Matawalle ya ce ganawar ta biyo bayan umarnin da shugaba kasa Muhammadu Buhari ya bayar inda ya ce duk masu ruwa da tsaki su nemo hanyar da za’a bi wajen kawo karshen ta’addanci.

‘Kun san kwanannan na gana da shugaba Muhammad Buhari akan matsalolin tsaro da muke fuskanta a jihar.

‘Daga cikin alkawarin da na yi masa na ce zan gana da masu ruwa da tsaki akan yadda za’a kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a jihar. Matsalar tsaro a Zamfara ta kasance damuwa ta tun kafin na zama gwamnan jihar, Na gode wa Allah da ya bani damar mulkar wannan jihar.

Abun bai yi dadi ba; an san fulanibda san zaman lafiya, sannan akwai kyakyawar alaka tsakanin mu da fulani kuma duk wani bafulatani mai bin doka baya jin dadin abin da ke faruwa a jihar Zamfara da wasu sassan kasar nan. An samu wasu bata gari da ke bata sunan Fulani. Na samu labari daga wasu garuruwan Fulani basa iya fita waje, saboda haka muna so mu dakatar da hakan.

Gwamnan ya kara da cewa dukkan wani nagartaccen bafulatani sai ya taimaka wajen dawo da kimar su da aka sani na zaman lafiya , hakuri da kuma fahimta. Kamar yadda ba fada lokacin rantsar da ni, ‘ba zan bari a ci gaba da kashe mutane ba a jihar. Na yi alkwarin yi wa kowa adalci sannann zan tabbatar da bin doka.

Za mu aika wa da majalisa kudirin yanke hukuncin kisa ga duk wanda muka kama yana garkuwa da mutane da masu basu bayanai. Ina da shirin shigo da irin ciyawa daga Chana wadda za’a baiwa fulani don taimaka musu wajen ciyar da dabbobijnsu. Ina da shirye shirye daban daban don ganin an shawo kan matsalar tsaro a jihar.
Zamu samar wa da fulani makiyaya kayan more rayuwa wanda ya hada da Asibitoci, makarantu, hanyoyi da sauran abubuwa.

Na kaddamar da shirin bayar da ilimi kyauta da harkar lafiya a fadin jihar. Ina da shirin samar da titina da cikin kauyuka amma idan ba zaman lafiya dukkan wadannan abubuwan ba zasu yiwu ba.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!