Connect with us

LABARAI

Hukumar Kwastam A Jihar Ogun Ta Tara Naira Bilyan 1.13, Ta Kwace Motoci 38

Published

on

Hukumar Kwastan shiyyar Ogun, ta ce ta tara Naira bilyan 1.131 a watan Mayu. Da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Talata, a hedikwatar hukumar da ke Idi-Iroko, kwanturolan shiyya na hukumar, Michael Agbara ya ce, a bisa adadin kudin da hukumar ta tara, har ta shige yawan abin da ya kamata ta tara a wata na Naira milyan 643.4, ta wuce hakan da Naira milyan 488.3.

Agbara ya kuma bayyana cewa, hukumar na su ta kuma kwace kayayyaki 103, da suka hada da motoci 38, buhunan shunkafa 7,030 da jarkokin man girki guda 372. A cewar shi, sashen yaki da ‘yan fasakwari na hukumar na shi sun kwace jarkunan man fetur guda 411, mashinan hawa guda uku, da kuma takalman sawa a kafa sabbi guda 1,835 da kuma tsaffi guda 264.

Agbara, ya bugi kirjin hukumar na shi ta hana ‘yan fasakwari sakat a shiyyar tasu, ta kuma rage wuraren bincikar ababen hawa a kan hanyar ta Idi-Iroko.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!