Connect with us

LABARAI

Kagame Ga Buhari: Akwai Abubuwan Da Suka Fi Yaki Da Rashawa Muhimmanci

Published

on

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame ya shaidawa shugaban kasa Buhari cewa; akwai abubuwan da suka fi yaki da da rashawa muhimmanci. Paul Kagame, ya shaidawa Buhari da sauran kasashen Afrika cewa; yaki da cin hanci da rashawa bai wadatu ba, akwai bukatar bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma wadatar da kasar, tare da muhimmantar da rayukan al’umma.

Shugaban Rwanda din ya bayyana hakan ne a taron da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya wato EFCC suka shirya a jiya Talata a birnin tarayya Abuja. Inda Kagame ya kuma taya shugaba Buhari murnar sake lashe zabe a karo na biyu. Ya kara da cewa; akwai bukatar Nijeriya ta yiwa kowa adalci domin kowa ya amfana daga yaki da cin hanci da rashawa da ake yi ta hanyar raba arzikin kasa ga kowa ba tare da nuna fifiko ba.

Inda kuma ya yi kira ga mahalarta taron da shugaban kasa Buhari da su tabbatar sun fito da hanyoyin bunkasa arzikin kasa a yayin da suke yaki da cin hanci ba kaiwa su himmatu da yaki da cin hancin ba.

Ya ce batun yaki da cin hanci da rashawa abu ne da za a iya nasara akan sa, domin yadda da cin hanci wani abu ne da yake zabi, ba wai abin da ba za a iya magance shi ba. Ya ce; masu mulki suna da karfin da za su iya magance shi. Ya ce; wannan muhimmin abu ne da ya kamata a lura da shi, idan ba haka ba zai zama bata lokaci a ci gaba da babatu akan batun.

 

 
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!