Connect with us

KASUWANCI

Kamfani Amurka Zai Zuba Jarin Dala Biliyan 10 Don Gina Layin Dogo Mai Sauri

Published

on

Mai kamfanin Ameri Metro Inc dake kasar Amurka Mista Shah Mathias, ya sanar da cewar, kamfanin sa a shirye yake ya zuba jarin sama da dala biliyan goma akan aikin layin dogo daga jihar Legas zuwa garin Kalaba da kuma Fatakwal.

Shah Mathias, ya sanar da hakan ne a hirar da manema labarai jim kadan bayan ya kaiwa ministan ma’aikatar sufuri Cif Rotimi Amaechi ziyara a Abuja inda yace, kamfanin nasa zai zuba dukkan kudin in har gwamnatin tarayya ta amince.

Mathias yaci gaba da cewa,“munzo nan ne don gabatar da maganar jirgin kasa mai gudu da kuma sauran ayyukan da muke gudanarwa, kuma manufar mu itace, gina layin dogo na zamani wadda zamu iya fara a ko wanne lokaci.”

A cewarsa, “a shirye muke mu zuba jari kashi dari bisa dari kuma an gaya mana cewar, aikin ya kai dala sama da biliyan goma, zamu gina sabbin layin dogo da kawo taragwanni.”

Ya bayyana cewar, “muna ganin zamu fara daga jihar Legas zuwa Kalaba da kuma Fatakwal haka a shirye muke mu karba daga kamfanin kasar China tunda sun kasa tara kudi.”

Mathias ya kara da cewa, kamfanin sa yana mayar da hankali ne akan jirgin kasa mai gudu don safarar fasinjoji da kayan su.

Ya sanar da cewar, kamfanin nasa ya yi ayyuka da dama na layin dogo a kasar Amurka kuma yana da kudi da karfin gudanar da ayyuakan layin dogo a Nijeriya.
Advertisement
Click to comment

labarai

Share This

Share this post with your friends!